DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 6-8
An Gwada Bangaskiyar ’Yan’uwa a Sabuwar Ikilisiya
Da alama an nuna bambanci ma gwauraye Helenawa da suka ci gaba da zama a Urushalima bayan sun yi baftisma. Shin hakan ya sa sun bar ikilisiyar ne ko kuma sun yi haƙuri suna jira har sai lokacin da Jehobah zai daidaita al’amarin?
Bayan da aka jefi Istifanus da duwatsu kuma aka daɗa tsananta ma Kiristoci, hakan ya sa Kiristoci da suke Urushalima sun yi gudun hijira zuwa wasu yankunan Yahudiya da kuma Samariya. Hakan ya sa sun yi sanyi a hidimarsu ne?
Jehobah ya taimaka wa ’yan’uwa a sabuwar ikilisiyar su jimre kuma su ci gaba da ƙaruwa.—A. M 6:7; 8:4.
KA TAMBAYI KANKA, ‘Me nake yi idan na fuskanci jaraba?’