12-18 ga Nuwamba
AYYUKAN MANZANNI 1-3
Waƙa ta 104 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“An Zuba Wa Ikilisiyar Kirista Ruhu Mai Tsarki”: (minti 10)
[Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Ayyukan Manzanni.]
A. M 2:1-8, 14, 37, 38, 41—Bayan da ruhu mai tsarki ya sauƙo musu, almajiran Yesu sun yi wa’azi da ya sa mutane 3,000 suka yi baftisma
A. M 2:42-47—Almajiran Yesu sun kula da baƙi da suka ci gaba da zama a Urushalima na ɗan lokaci bayan sun yi baftisma kuma hakan ya ƙarfafa bangaskiyar baƙin (mwbr18.11-HA an ɗauko daga w86 12/1 29 sakin layi na 4-5, 7)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
A. M 3:15—Me ya sa aka kira Yesu “Tushen Rai”? (mwbr18.11-HA an ɗauko daga it-2 61 sakin layi na 1)
A. M 3:19—Ta yaya wannan ayar ta bayyana yadda Jehobah yake gafarta wa mai zunubi da ya tuba? (cl 265 sakin layi na 14)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A. M 2:1-21
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Jawabi: (minti 6 ko ƙasa da hakan) it-1-E 129 sakin layi na 2-3—Jigo: Me Ya Sa Aka Mai da Gurbin Yahuda Iskariyoti Amma Ba A Mai da Gurbin Manzanni Masu Aminci da Suka Mutu Ba?
RAYUWAR KIRISTA
“Mu Yi Wa’azi da Haɗin Kai A Yankuna da Ake Yaruka da Yawa”: (minti 15) Tattaunawa da mai kula da hidima zai yi. Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi. Idan ikilisiyarku tana yin wa’azi a yankunan da ake yaruka dabam-dabam, ka bayyana tsarin da ikilisiyarku take bi a yin hakan.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 15 sakin layi na 18-23 da akwatin da ke shafi na 180
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 68 da Addu’a