RAYUWAR KIRISTA
Ƙauna Ce Alamar Kiristoci Na Gaskiya—Ku Yi Murna da Gaskiya
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Wajibi ne mu gaya wa mutane game da nufin Allah kamar yadda Yesu ya yi. (Yoh 18:37) Ban da haka, wajibi ne mu riƙa murna da gaskiya da faɗin gaskiya da kuma yin abubuwan da suke da kyau duk da cewa muna rayuwa a duniyar da ba a yin hakan.—1Ko 13:6; Fib 4:8.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
Kada ka saurari ko ka yaɗa gulma don ka ɓata sunan wani.—1Ta 4:11
Kada ka yi murna sa’ad da wani ya shiga cikin matsala
Ka riƙa yin abubuwan da za su taimaka ko ƙarfafa mutane
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KU YI MURNA DA GASKIYA, BA DA RASHIN ADALCI BA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Ta yaya Debbie ta yi murna da rashin adalci?
Mene ne Alice ta faɗa da ya taimaka wa Debbie ta canja tunaninta?
Waɗanne abubuwa masu kyau ne za mu iya tattaunawa da mutane?
Ka yi murna da gaskiya ba da rashin adalci ba