DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 14-16
Kwatancin Yesu Game da Mubazzari
Wasu darussa da muka koya daga kwatancin.
Yana da kyau mu riƙa kasancewa tare da ’yan’uwanmu Kiristoci kuma mu bi ja-gorancin Ubanmu mai ƙauna
Idan mun bar ƙungiyar Jehobah, ya kamata mu dawo domin muna da tabbaci cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta mana
Ya kamata mu bi misalin Jehobah ta wajen marabtar ’yan’uwa da suka tuba kuma suka dawo ƙungiyar Jehobah