Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Yuli p. 3
  • Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Kunsa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Kunsa?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ka Kalli Abubuwan Da Ke “Baya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Abin da Ke Janyo Zunubi da Mutuwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Aikinmu Na Ba da Agaji
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?
    Tambayoyin Matasa
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Yuli p. 3

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 8-9

Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Ƙunsa?

9:62

Idan manomi yana son ya ja kunya a miƙe, yana bukatar ya mai da hankalinsa a kan aikin da yake yi kuma kada ya bar abubuwan da ke bayansa su raba hankalinsa. Hakazalika, bai kamata Kirista ya bar abubuwan da ya bari a baya su raba hankalinsa ba.​—Fib 3:13.

In mun shiga matsala, hakan zai iya sa mu tuna da abubuwan da muke ganin mun mora a dā wataƙila kafin mu soma bauta wa Jehobah. Idan muna tunawa da hakan, za mu ga kamar mun fi jin daɗi a dā kuma mu manta da wahalar da muka sha a lokacin. Abin da ya faru da Isra’ilawa ke nan sa’ad da suka bar ƙasar Masar. (L.Ƙi 11:​5, 6) Idan muka ci gaba da tuna baya, za mu iya soma marmarin yin irin rayuwar da muka bari. Don haka, zai fi kyau mu mai da hankali ga albarka da muke samu a yanzu da waɗanda za mu samu a Mulkin Allah!​—2Ko 4:​16-18.

Wani manomi ya mai da hankali a kan kunya da yake ja, bai damu da abubuwa da ke bayansa ba
    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba