16-22 ga Yuli
LUKA 10-11
Waƙa ta 100 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kwatanci Game da Basamariye Mai Kirki”: (minti 10)
Lu 10:29-32—Da farko wani Firist ya zo ya wuce, bayan shi sai wani daga zuriyar Lawi ma ya wuce, dukansu sun ƙi su taimaka wa Bayahuden da ɓarayi suka yi masa dūka [Ka saka bidiyon Luka 10:30 a nwtsty.] (w02 9/1 23-24 sakin layi na 14-15)
Lu 10:33-35—Wani Basamariye ya nuna ma Bayahuden ƙauna (duba bayanin Lu 10:33, 34 a nwtsty)
Lu 10:36, 37—Mu riƙa ƙaunar kowa da kowa, ba kawai waɗanda suke da arziki kamar mu ko waɗanda launin fatarmu ko ƙabilarmu ko kuma ƙasarmu ɗaya ba (w98 7/1 31 sakin layi na 2)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Lu 10:18—Me Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa mabiyansa guda 70 cewa: “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya”? (duba bayanin a nwtsty; w08 3/15 31 sakin layi na 11)
Lu 11:5-9—Wane darasi ne muka koya game da addu’a a kwatancin da Yesu ya yi game da wani mutum mai naciya? (duba bayanin a nwtsty)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Lu 10:1-16
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Maigidan ya ƙi saurarar wa’azin kuma ya ba da hujjar da mutane a yankinku suka saba bayarwa.
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Maigidan ya gaya maka cewa yana cin abinci.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
RAYUWAR KIRISTA
“Kada Mu Saka Hannu a Harkokin Siyasa (Mi 4:2)”: (minti 15) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 10 sakin layi na 9-15 da akwatin da ke shafi na 114
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 146 da Addu’a