DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 39-43
Jehobah Zai Sāka wa Kowa Bisa ga Ayyukansa
Zadakiya ya ƙi bin umurnin da Jehobah ya ba shi cewa ya miƙa wuya ga Babila
39:4-7
An kashe yaran Zadakiya a idonsa. Shi kuma an ɗaure shi da sarƙa kuma an saka shi a kurkuku har mutuwarsa a Babila
Ebed-melek ya dogara ga Jehobah kuma ya taimaka wa Irmiya
39:15-18
Jehobah ya yi alkawari cewa zai kāre Ebed-melek a lokacin da za a halaka mutanen Yahuda
Kafin a halaka Urushalima, Irmiya ya yi shekaru da yawa yana wa’azi da gaba gaɗi
40:1-6
Jehobah ya kāre Irmiya a lokacin da aka halaka Urushalima kuma ya sa Babiloniyawa su saki Irmiya