DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 35-38
Ebed-melek Misali Ne Na Ƙarfin Hali da Kuma Alheri
Ebed-melek, wanda ma’aikaci ne a fādar Sarki Zadakiya ya nuna halaye masu kyau
38:7-13
Ya nuna ƙarfin hali da basira ta wajen gaya wa Sarki Zadakiya abin da ya faru da Irmiya kuma ya fitar da shi daga rijiyar
Ya nuna alheri ta wajen saka tsumma mai laushi a hammatar Irmiya don kada igiyar ta ji masa rauni