RAYUWAR KIRISTA
Matasa—Kada Ku Yi Jinkirin Shigan “Ƙofa Mai-Faɗi”
Za mu iya yin tunani cewa ba za mu taɓa shaida “miyagun kwanaki” da tsufa ke kawowa a wannan duniyar Shaiɗan ba. (M. Wa 12:1) Idan kai matashi ne, shin zai dace ka ce za ka faɗaɗa hidimarka a nan gaba tun da yake kana da sauran shekaru da yawa kafin ka tsufa?
“Sa’a da tsautsayi” suna iya shafar kowannenmu, har da matasa. (M. Wa 9:11, Littafi Mai Tsarki) “Ba ku san abin da za ya faru gobe ba.” (Yaƙ 4:14) Saboda haka, kada ku ƙi faɗaɗa hidimarku ba gaira ba dalili. Ku shiga “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” yanzu da yake kuna da zarafin yin haka. (1Ko 16:9) Ba za ku yi da-na-sani ba.
Wasu maƙasudai da za ku iya kafawa:
Yin wa’azi a wani yare
Hidimar majagaba
Halartar makarantun ƙungiyar Jehobah
Hidimar gine-gine
Hidimar Bethel
Hidimar mai kula mai ziyara