DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAI-WA’AZI 7-12
“Ka Tuna da Mahaliccinka . . . a Cikin Kwanakin Ƙuruciyarka”
Ka tuna da Mahaliccinka ta wajen yin amfani da ƙwarewarka don bauta masa sa’ad da kake matashi
12:1, 13
Matasa da yawa suna iya bi da ƙalubale da kuma aiki mai wuya domin suna da koshin lafiya da ƙarfi
Ya kamata matasa su yi amfani da lokacinsu da kuma ƙarfinsu a hidimar Jehobah kafin su tsufa kuma su ƙasa yin hakan
Sulemanu ya yi amfani da fasahar magana wajen kwatanta lokacin tsufa
12:2-7
Aya ta 3: ‘Yan matan da ‘suke leƙa ta cikin sakata sun duhunta’
Rashin gani sosai
Aya ta 4: ‘Mata masu-rairawa sun yi shiru’
Rashin ji sosai
Aya ta 5: ‘Ya’yan itace “sun lalace”
Raguwar marmarin abinci