Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/15 p. 2
  • “Ku Ƙaunaci Dukan ’Yan’uwa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Ƙaunaci Dukan ’Yan’uwa”
  • Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Makamantan Littattafai
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Yi Zaman Bangaskiya Ba Na Ganin Ido ba!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Bangaskiya​—Tana Sa Mu Kasance da Karfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2015
km 12/15 p. 2

“Ku Ƙaunaci Dukan ’Yan’uwa”

An rubuta waɗannan kalmomin da ke sama kusan shekaru dubu biyu da suka shige. (1 Bit. 2:17) Amma yanzu ne ya kamata mu yi amfani da su fiye da dā! Ta yaya za mu yi ƙaunar dukan ’yan’uwa da ke faɗin duniya? A wannan duniyar da babu ƙauna, ta yaya za mu tabbata cewa ƙaunarmu ba ta yi sanyi ba? (Mat. 24:12) Ka mai da hankali ka ga ko za ka iya ba da amsa ga waɗannan tambayoyi na gaba sa’ad da kake kallon bidiyon nan Dukan ’Yan’uwanmu a Faɗin Duniya. (1) Yaushe ne mutum yakan shiga cikin iyalinmu na faɗin duniya? (2) Waɗanne abubuwa uku ne Shaidun Jehobah ke yi a duk faɗin duniya? (3) Ta yaya ’yan’uwanmu suke ƙoƙari wajen yin wa’azi a (a) dajin Alaska (b) tashar jiragen ruwa da ke ƙasar Turai da kuma (c) dajin Peru? (4) Me ya sa bai dace mu raina yin wa’azi ba? (5) Ka ba da misalan da suka nuna yadda Shaidun Jehobah suka ta’azantar da kuma tallafa wa juna (a) bayan girgizar ƙasa (b) bayan guguwa da kuma (c) a lokacin yaƙi? (6) A waɗanne hanyoyi ne dukanmu za mu nuna cewa muna ƙaunar juna? (Yoh. 13:35) (7) Ta yaya muke amfana idan muka yi aiki tare don mu gina Majami’un Mulki? (8) Ta yaya ’yan’uwanmu a ƙasar Turai da Rasha suka ci gaba da ayyukan ibada sa’ad da aka saka wa aikinmu takunkumi? (9) Wane ƙoƙari ne ’yan’uwanmu suke yi don su riƙa halartan taro, kuma me ya sa? (10) Ta yaya wannan bidiyon zai ƙarfafa ka ka ci gaba da (a) halartan taro tare da ’yan’uwanka da haɗin kai, (b) taimaka wa ’yan’uwa a lokacin da suka faɗa bala’i, da kuma (c) yin wa’azi da aminci daidai ƙarfinka? (11) Ta yaya za mu yi amfani da wannan bidiyon a wa’azi kuma a yaushe za mu yi hakan?

Ainihin dalilin da ya sa muke wannan ƙungiyar shi ne ƙaunarmu ga Jehobah. Shi ya sa muke son mu koya game da shi kuma mu koyar da wasu ma. Kuma muna ƙaunar waɗanda Jehobah yake ƙauna. Ba ma bukatar Jehobah ya gode mana idan muka taimaka wa waɗanda suka faɗa cikin bala’i. Maimakon haka, muna gode wa Jehobah don wannan ƙungiyar babbar kyauta ce. Da yake wannan muguwar duniyar ta kusan ƙarewa, zai dace mu ci gaba da nuna ƙauna ga dukan ’yan’uwanmu a faɗin duniya!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba