Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 26 Oktoba, 2015.
Ta yaya labarin da ke 2 Sarakuna 13:18, 19 ya kwatanta muhimmancin kasancewa da himma da kuma bauta wa Allah da zuciya ɗaya? [7 ga Satumba, w10 4/15 shafi na 26 sakin layi na 11]
Wane sarki ne yake sarauta a Isra’ila a lokacin da Yunana ya yi hidima a matsayin annabi, kuma mene ne 2 Sarakuna 14:23-25 ya koya mana game da hidimar da ya yi? [7 ga Satumba, w09 1/1 shafi na 25 sakin layi na 4]
Ta yaya Ahaz ya nuna cewa bai amince da abin da Allah ya tura annabi Ishaya ya faɗa ba, kuma wace tambaya ce ya kamata mu yi sa’ad da muke yanke shawara? (2 Sar. 16:7) [14 ga Satumba, w13 11/15 shafi na 17 sakin layi na 5]
Wace dabara irin ta Rabshakeh ce maƙiyan bayin Allah suke amfani da ita a yau, kuma mene ne zai taimaka mana mu guji ra’ayinsu? (2 Sar. 18:22, 25) [14 ga Satumba, w10 7/15 shafi na 13 sakin layi na 3-4]
Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Allah ba zai ƙyale mugunta ta ci gaba har abada ba? (2 Sar. 19:35, 36) [21 ga Satumba,w10 11/15 shafi na 26 sakin layi na 12]
Ta yaya labarin da ke 2 Sarakuna 24:3, 4 ya nuna cewa Jehobah yana daraja jinin marasa laifi? [28 ga Satumba, w05 8/1 shafi na 31 sakin layi na 1]
Waɗanne abubuwa uku ne Jabez ya roƙi Jehobah ya yi masa, kuma mene ne wannan ya koya mana game da addu’a? (1 Laba. 4:9, 10) [5 ga Oktoba, w11 1/1 shafi na 10]
Ta yaya sakamakon yaƙin da aka ambata a littafin 1 Labarbaru 5:18-22 ya ƙarfafa mu mu ci gaba da hidimar Allah da gaba gaɗi? [12 ga Oktoba, w05 10/1 shafi na 29 sakin layi na 7]
Mene ne ya taimaki Dauda ya fahimci kuma ya bi dokar Jehobah game da jini, kuma mene ne za mu iya koya daga misalinsa? (1 Laba. 11:17-19) [19 ga Oktoba, w12 11/15 shafuffuka na 6-7 sakin layi na 12-14]
Wane sakaci ne Dauda ya yi sa’ad da yake ƙoƙarin kawo sunduƙin alkawari zuwa Urushalima, kuma wane darasi za mu koya daga wannan labarin? (1 Laba. 15:13) [26 ga Oktoba, w03 5/1 shafi na 16 sakin layi na 11-13]