Yadda Za Mu Ratsa Zukatan Mutane
1. Ta yaya koyarwar Yesu ta ratsa zukatan masu sauraronsa?
1 Yesu ya ratsa zuciyar mutanen da ya koyar. Akwai lokacin da zukatan almajiransa suke “ƙuna” don ya bayyana musu Nassosi a hanyar da suka fahimta sosai. (Luk. 24:32) Da yake daga zuciya ake yin biyayya ga Allah, ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su canja salon rayuwarsu?—Rom. 6:17.
2. Ta yaya basira da hikima za su taimaka idan muna so mu ratsa zukatan mutane?
2 Ka Nuna Basira da Kuma Hikima: Gaya wa wasu mutane abin da ya dace da wanda bai dace ba kawai, ba zai motsa su su ɗauki matakin da ya dace ba. Babu shakka, idan kana yawan kushe abubuwan da suka gaskata ta wajen karanta musu ayoyi da yawa, ba za su so su saurare ka ba. Idan har muna so mu taimaka wa mutane, zai dace mu san dalilin da ya sa suka gaskata da wani abu kuma suka ɗauki wani mataki. Idan muka kasance da basira kuma muka yi masa tambayoyin da suka dace, hakan zai iya sa ya gaya mana ainihin abin da yake zuciyarsa. (Mis. 20:5) Yin hakan zai taimaka mana mu zaɓi bayanin da ke Kalmar Allah da zai iya ratsa zuciyarsa. Saboda haka, ya kamata mu nuna mun damu da mutumin kuma mu kasance da haƙuri. (Mis. 25:15) Ƙari ga haka, zai dace mu tuna cewa yadda mutane suke samun ci gaba a ƙungiyar Jehobah ya bambanta. Suna bukatar lokaci don ruhun Jehobah ya yi tasiri a kan tunaninsu da kuma ayyukansu.—Mar. 4:26-29.
3. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su kasance da halaye masu kyau?
3 Ka Taimaka Musu Su Kasance da Halaye Masu Kyau: Labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna nagartar Jehobah da ƙaunarsa za su taimaka wajen koyar da mutane su zama da halayen kirki. Za mu iya yin amfani da nassosi kamar su Zabura 139:1-4 ko Luka 12:6, 7 don mu nuna yadda Allah ya damu da kowanenmu. Idan mutane suka san muhimmancin nagartar Jehobah, ƙaunarsu da kuma ibadarsu ga Jehobah za ta yi ƙarfi sosai. (Rom. 5:6-8; 1 Yoh. 4:19) Ƙari ga haka, idan suka fahimta cewa halinsu zai iya shafan Jehobah, hakan zai ba su kuzarin yin abin da zai faranta masa rai kuma ya sa a ɗaukaka shi.—Zab. 78:40, 41; Mis. 23:15.
4. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ‘yancin mutane sa’ad da muke koya musu Littafi Mai Tsarki?
4 Allah ba ya tilasta wa mutane su bauta masa. Maimakon haka, yana nuna wa mutane hikimar bin shawararsa. (Isha. 48:17, 18) Idan muka koyar da mutane a hanyar da ta dace har muka ratsa zuciyarsu, hakan zai nuna cewa muna yin koyi da Jehobah. Mutane za su yi canja salon rayuwarsu da zuciya ɗaya idan suka san muhimmancin yin hakan. (Rom. 12:2) Ƙari ga haka, hakan yana jawo su kusa da Jehobah wanda yake “auna zukata.”—Mis. 17:3.