Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah! a Haɗuwa ta Farko
Muhimmancinsa: Kafin mu yaɗa bishara, ya wajaba mu iya koyar da Kalmar Allah sosai. (Mat. 28:19, 20) Dukanmu za mu iya koyar da gaskiya yadda ya dace ta wajen yin amfani da kayayyakin aiki da aka tanadar mana. An tsara wannan ƙasidar Albishiri Daga Allah! musamman domin ta taimaka mana mu koya wa mutane gaskiya. Hakika, za mu iya yin amfani da ita domin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a haɗuwa ta farko.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Ka yi addu’a don ka kasance da muradin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani kuma ka ƙware wajen koyar da Kalmar Allah.—Filib. 2:13.
Ka nemi lokaci don ka koyi gabatarwar sa’ad da kuke ibada ta iyali ko kuma kake nazari kai kaɗai. Yin hakan zai taimaka maka ka yi magana da gaba gaɗi kuma ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutum a haɗuwa ta farko.