Tsarin Ayyuka Makon 4 Ga Mayu
MAKON 4 GA MAYU
Waƙa ta 68 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 24 sakin layi na 1-10 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 1-3 (minti 8)
Na 1: 2 Sama’ila 2:24-32 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Amfanin Zama Masu Sauƙin Hali da Kuma Haƙuri (minti 5)
Na 3: Alkawuran Littafi Mai Tsarki da Za Su Cika Nan Ba da Daɗewa Ba—igw 16 sakin layi na 4 zuwa 17 sakin layi na 1 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: Ku zama masu hikima ta yin “amfani da lokaci” a hanya mafi inganci.—Afis. 5:15, 16, Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 43
Minti 10: Bukatun ikilisiya. Za a iya haɗa da gwaji a kan yadda za a ba da mujallu.
Minti 5: Littattafan da Za Mu Ba Mutane a Watan Mayu da Yuni. Tattaunawa. Ka tattauna abin da ke cikin littattafan da za a ba mutane. Bayan haka, ka sa a yi gwaji a kan yadda za a ba da littattafan.
Minti 15: Yin Hidima a Yankunan da Ba A Yawan Yin Wa’azi Hanya Ce Mai Kyau na Yin Amfani da Lokacinmu! Dattijo ne zai tattauna wannan sashen. Idan zai yiwu, a ba dattijon da ya taɓa wa’azi a yankunan da ba a yawan wa’azi a cikinsu. Ka kunna bidiyon nan Yin Wa’azi a Yankin da Shaidun Jehobah Ba Sa Yawan Zuwa Wa’azi—Ostareliya. (Ka shiga dandalin jw.org/ha kuma ka duba shafin nan GAME DA MU > AYYUKA.) Ka tattauna yadda iyalin da aka nuna a bidiyon nan suka amfana daga yin wa’azi a yankin da ba a yawan yin wa’azi. Ka gana da wani a cikin ikilisiyar da ya taɓa yin irin wannan fannin wa’azi. Ta yaya ya shafi dangantakarsu a cikin iyali da hidimarsu da kuma ibadarsu? Waɗanne shirye-shirye ne suka yi? Idan akwai wani mai shela da yake so ya yi wa’azi a irin wannan yankin, dattawa za su yi farin cikin taimaka masa. Ka nanata cewa yin wa’azi a yankunan da ba a yawan yin wa’azi hanya ce mai kyau ta yin amfani da lokacinmu.
Sabuwar waƙa “Teach Them to Stand Firm” da Addu’a
Tunasarwa: Don Allah a saka wa masu sauraro sabuwar waƙar sau ɗaya don su saurara, bayan haka, sai su rera waƙar tare.