Tsarin Ayyuka na Makon 6 ga Afrilu
MAKON 6 GA AFRILU
Waƙa ta 124 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 22 sakin layi na 18-22 da akwatin da ke shafi na 228 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sama’ila 16-18 (minti 8)
Na 1: 1 Sama’ila 18:17-24 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Allah Ne Yake Jawo wa ’Yan Adam Wahala?—igw 14 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Shugabanni Masu Basira Suke Yaba wa Shaidun Jehobah?—Rom. 13:3 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: ‘Ku Zama Shiryayyu don Kowane Kyakkyawan Aiki.’—Tit. 3:1.
Waƙa ta 85
Minti 10: Ku ba da Mujallu a Watan Afrilu. Tattaunawa. Da farko, ka sa a yi gwaji a kan yadda za mu iya ba da mujallunmu bisa ga gabatarwar da aka bayar. Sai ka yi kalami a kan kowace gabatarwar.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim ma? Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga bin shawarar nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Samun Wani da Za Ku Riƙa Kai wa Mujallu a Kai a Kai.” Ka ba masu sauraro dama su faɗi labarai masu daɗi da suke da shi.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Waƙa ta 106 da Addu’a