Ku Yi Amfani da Dandalinmu Sa’ad da Kuke Wa’azi—“An Amsa Tambayoyin Littafi Mai Tsarki”
A ƙarƙashin sashen “Koyarwar Littafi Mai Tsarki” a dandalin jw.org, akwai sashen nan “An Amsa Tambayoyin Littafi Mai Tsarki.” Idan mun karanta tambayoyin da ake yawan yi kuma mun san amsoshinsu sosai, za mu iya gaya ma waɗanda suka yi waɗannan tambayoyin yadda za su sami amsoshin Littafi Mai Tsarki a dandalinmu ko mu nuna musu yadda za su shiga dandalin. Za mu kuma iya soma tattaunawa da mutane ta wurin yi musu waɗannan tambayoyin. Za mu iya yi wa mai gidan wata tambaya da ke damun mutane a yankin gaba ɗaya, mu saurari nasa ra’ayin, sa’an nan mu gaya masa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kan batun bisa ga bayanin da muka samo a dandalin jw.org. Bayan haka, za mu iya gaya masa inda muka samo bayanin ko kuma mu nuna masa dandalin. Wani abu kuma da za mu iya yi shi ne, mu shiga dandalin, mu nuna masa amsar kuma mu ba shi ya karanta. Matar wani mai kula mai ziyara ta saba yin hakan, kuma ta sami sakamako mai kyau. Ga abin da take faɗa: “Mutane da yawa suna tunani, ‘Shin wahalar da muke sha a yau nufin Allah ne?’ Za ka so ka san amsar wannan tambayar a cikin sakan 51 kawai?” Sai ta kunna masa amsar tambayar da ta saukar cikin na’urarta don ya saurara. Sa’an nan ta kammala ta wajen gabatar wa mai gidan babi na 11 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?