Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 25 ga Agusta, 2014.
Mene ne ya nuna cewa ba Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa ne kawai zai buɗe wa Isra’ilawa hanyar samun rai madawwami ba? [7 ga Yuli, w09 8/15 shafi na 6 sakin layi na 14]
Mene ne muka koya daga dokar da ke Levitikus 19:2, kuma me ya sa zai dace mu ƙoƙarta wajen bin dokar? [7 ga Yuli, w09 7/1 shafi na 9 sakin layi na 5]
Mene ne za mu iya koya daga ƙa’idar yin kala a dā? (Lev. 19:9, 10) [7 ga Yuli, w06 7/1 shafi na 10 sakin layi na 13]
Me ya sa za a ce dokar “ido domin ido” ba ta ƙarfafa ramuwa ba? (Lev. 24:19, 20) [14 ga Yuli, w09 10/1 shafi na 22 sakin layi na 3-4]
A waɗanne yanayi ne ba zai dace Ba’Isra’ile ya karɓi ruwa idan ya ba da rance ba, kuma a wane yanayi ne zai iya yin haka? (Lev. 25:35-37) [21 ga Yuli, w04 7/1 shafi na 31 sakin layi na 4]
Me ya sa ake yawan ambata ƙabilu 12 na Isra’ila, alhali ƙabilu 13 ake da shi? (Lit. Lis. 1:49, 50) [28 ga Yuli, w08 7/1 shafi na 27]
Wane darasi game da mutunta tsofaffi ne za mu iya koya daga abin da aka rubuta game da hidimar Lawiyawa a Litafin Lissafi 8:25, 26? [11 ga Agusta, w04 8/1 shafi na 29 sakin layi na 8]
Me ya sa Isra’ilawa suka kasance da halin gunaguni bayan da aka fitar da su daga ƙasar Masar ta hanyar mu’ujiza, kuma wane darasi mai kyau ne za mu iya koya daga wannan labarin? (Lit. Lis. 11:4-6) [18 ga Agusta, w95 3/1 shafi na 28 sakin layi na 10]
Mene ne za mu iya koya daga matakin da Musa ya ɗauka sa’ad da Eldad da Medad suka fara yin annabci? (Lit. Lis. 11:27-29) [18 ga Agusta, w04 8/1 shafi na 30 sakin layi na 9]
Wace ƙa’ida ce za mu iya koya daga dokar da aka ba Isra’ilawa cewa “su sa tuntaye a shafin rigassu”? (Lit. Lis. 15:37-39) [25 ga Agusta, w04 8/1 shafi na 31 sakin layi na 2]