Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/14 pp. 2-7
  • Shekaru Ɗari da Shelar Mulkin!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shekaru Ɗari da Shelar Mulkin!
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • 1914-2014 Shekaru Ɗari da Kafa Mulkin Allah!
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Me Yesu Ya Cim ma a Sarautar da Ya Yi na Shekara 100?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Ya Sa Zai Dace Ka San Game da Mulkin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Masu Yin Wa’azi​—Masu Yin Wa’azi Sun Ba da Kansu da Yardan Rai
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 8/14 pp. 2-7

Shekaru Ɗari da Shelar Mulkin!

1. Mene ne aka ƙarfafa bayin Jehobah su yi kusan shekaru 100 da suka gabata?

1 “Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma mulkinsa.” Da waɗannan kalmomi masu motsawa da Ɗan’uwa Rutherford ya furta kusan shekaru ɗari da suka gabata, an ƙarfafa bayin Jehobah su yi shelar Mulkin Allah a faɗin duniya. Babu shakka, abin da muka yi ke nan! Kamar Kiristoci na farko, mu ma mun yi shelar bisharar Mulkin ga “dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Mene ne muka cim ma sa’ad da muka yi shelar Mulkin Allah a cikin shekaru ɗari da suka gabata? Yayin da Mulkin yake gab da cika shekaru ɗari, ta yaya za mu ci gaba da yin wa’azinsa?

2. Ta yaya littattafanmu suke yin shelar Mulkin Allah?

2 Tuna Baya: A cikin shekaru da yawa, littattafanmu sun yi shelar Mulkin Allah. Tun shekara ta 1939, jigon mujallarmu ta Hasumiyar Tsaro shi ne: Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah. Wannan mujallar tana bayyana Mulkin Allah da kuma abubuwan da Mulkin zai cim ma. Mujallar Awake! ma tana nuna cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin ’yan Adam. Saboda haka, ya yi kyau cewa waɗannan ne mujallun da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a duniya!—R. Yoh. 14:6.

3. Waɗanne hanyoyi ne muka ƙirƙiro don yin shelar Mulkin?

3 Bayin Jehobah sun ƙirƙiro hanyoyi da yawa na yin shelar Mulkin Allah. A farko farko, mun yi amfani da motoci masu lasifika da shirye-shiryen rediyo da kuma garmaho. Waɗannan hanyoyin sun taimaka mana wajen yaɗa bishara a wurare da yawa a lokacin da masu shelar Mulki ba su yi yawa ba. (Zab. 19:4) A kwanan nan, mun wallafa abubuwa da yawa a dandalin jw.org kuma hakan ya taimaka wajen sanar da miliyoyin mutane game da Mulkin, har da waɗanda suke ƙasashen da ba a bari mu bauta wa Jehobah a sake.

4. Waɗanne hanyoyi na musamman ne muka taɓa amfani da su?

4 Shaidun Jehobah sun yi amfani da wasu hanyoyi na musamman don yaɗa bisharar Mulkin. Alal misali, ƙari ga yin wa’azi gida-gida, mun soma wa’azi a wuraren da ake samun jama’a kamar a kasuwa da tashar motoci, kuma mun soma yin hakan ne a tsakanin shekara ta 1994 da 1996. A kwanan nan, mun tsara hanya ta musamman na yin wa’azi a inda jama’a suke a manyan birane. Ƙari ga haka, ikilisiyoyi da yawa suna yin wa’azi ga jama’a a yankinsu ta wajen ajiye amalanke ko kuma tebura ɗauke da littattafai kusa da wuraren da jama’a suke yawan bi. Amma, har ila wa’azi gida-gida ne ainihin hanyar da muka fi yin wa’azi game da Mulkin.—A. M. 20:20.

5. Za mu sami damar yin me a sabuwar shekarar hidima da za a shiga?

5 Hangen Gaba: ’Yan’uwa da yawa za su soma hidimar majagaba a sabuwar shekarar hidima da za a shiga a watan Satumba. Kai ma za ka so ka yi hakan? Idan hakan ba zai yiwu ba, za ka iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a loto-loto? Ko da ka yi hidimar majagaba ko a’a, Jehobah zai albarkace ka saboda sadaukarwar da ka yi don yin shelar Mulkin.—Mal. 3:10.

6. Me ya sa watan Oktoba 2014 zai zama wata na musamman?

6 Za a cika shekara 100 da kafa Mulkin Allah a watan Oktoba 2014. Saboda haka, Hasumiyar Tsaro na wa’azi na watan za ta mai da hankali a kan Mulkin Allah, kuma hakan ya dace. Ka yi ƙoƙari sosai ka rarraba wannan mujallar ga mutane da yawa. Yayin da muke sauraron abin da zai faru a gaba, bari kowannenmu ya ci gaba da yin shelar ‘bisharar Mulkin Allah’ ga dukan waɗanda za su saurara.—A. M. 8:12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba