Yaya Jehobah Yake Ɗauka Na?
1. Me ya sa aka kwatanta Littafi Mai Tsarki da madubi?
1 Sau nawa kake kallon madubi? Yawancinmu mukan yi hakan kowace rana domin yana taimaka mana mu ga inda muke bukatar gyara a adonmu. An kwatanta Littafi Mai Tsarki da madubi. Yin karatun Kalmar Allah yana sa mu ga abin da Jehobah yake gani a duk lokacin da ya kalle mu, wato, abin da ke zuciyarmu. (1 Sam. 16:7; Yaƙ. 1:22-24) Kalmar Allah tana iya ‘gane tunanin zuciya da nufe-nufenta.’ (Ibran. 4:12) Ta yaya karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kanta kowace rana za su taimaka mana mu gano inda muke bukata mu yi gyara a rayuwarmu don mu zama ƙwararrun masu wa’azi?—Zab. 1:1-3.
2. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu bincika kanmu?
2 Ka Yi Amfani da Kalmar Allah a Matsayin Madubi: Labaran bayin Jehobah masu aminci a cikin Littafi Mai Tsarki suna bayyana mana irin halayen da Jehobah yake so. Alal misali, Dauda ya nuna himma don sunan Allah. (1 Sam. 17:45, 46) Ishaya ya sadaukar da kansa kuma ya yi wa’azi da gaba gaɗi a yankin da mutane ba sa cika sauraro. (Isha. 6:8, 9) Yesu yana ƙaunar Ubansa na sama sosai, shi ya bai ɗauki yin wa’azi a matsayin nawaya ba. A maimakon haka, ya ɗauke shi a matsayin hidima mai ƙayatarwa da kuma gamsarwa. (Yoh. 4:34) Kiristoci a ƙarni na farko sun yi wa’azi da himma, sun dogara ga Jehobah kuma sun ƙudurta cewa ba za su taɓa ja da baya ba. (A. M. 5:41, 42; 2 Kor. 4:1; 2 Tim. 4:17) Yin bimbini a kan irin misalan nan zai taimaka mana mu bincika kanmu da niyyar kyautata ibadarmu.
3. Me ya sa bai kamata mu yi jinkirin yin gyara da suka dace a rayuwarmu ba?
3 Ka Yi Gyara: Hakika, idan muka kalli madubi kuma muka ƙi mu yi gyarar da muke bukata, mun yi aikin banza ke nan. Za mu iya roƙon Jehobah ya taimaka mana mu bincika kanmu da kyau don mu yi gyarar da muke bukata mu yi. (Zab. 139:23, 24; Luk 11:13) Tun da yake lokaci ya ƙure ma wannan zamanin kuma rayukan mutane na cikin haɗari, bai kamata mu yi jinkirin yin gyarar da suka dace a rayuwarmu ba.—1 Kor. 7:29; 1 Tim. 4:16.
4. Me zai faru da mutumin da ya karanta Kalmar Allah kuma ya yi gyarar da yake bukata ya yi?
4 Jehobah yana kallon zuciyar mutum ne kuma a gare shi, hakan ya fi siffarsa muhimmanci. (1 Bit. 3:3, 4) Me zai faru da mutumin da ya karanta Kalmar Allah kuma ya yi gyarar da ta dace? Tun da yake shi “ba mai-ji wanda ke mantawa ba ne, amma mai-yi ne wanda ke aikatawa, wannan zai zama mai-albarka a cikin aikinsa.” (Yaƙ. 1:25) Hakika, za mu yi farin ciki kuma mu zama ƙwararrun masu wa’azi domin muna “juya [‘nuna,’ Littafi Mai Tsarki] darajar Ubangiji kamar madubi.”—2 Kor. 3:18.