Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/14 p. 7
  • Ku Ɗauki Mataki Nan da Nan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Ɗauki Mataki Nan da Nan
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Akwatin Tambaya
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Dandalinmu na Intane—An Tsara Shi Ne don ’Yan’uwa da Kuma Wasu Su Amfana
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43)
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 6/14 p. 7

Ku Ɗauki Mataki Nan da Nan

Tun daga lokacin da aka ƙaddamar da Yanar gizonmu da aka canja mata tsari, yawan mutanen da ke cika fom a dandalinmu don a yi nazari da su ya ƙaru sosai. Sabuwar hanyar yin wa’azi a inda akwai jama’a ma ta sa an sami ƙarin mutanen da suke so a yi nazari da su. Ofishin reshe yana ɗaukan mataki a kan wannan batun nan da nan. Alal misali, idan mutumin ya ba da sunansa ta dandalin jw.org ne, sai ofishin reshe ya sanar da dattawan da ke yankin mutumin cikin kwana biyu. Amma rahotanni daga yankuna da dama sun nuna cewa ba a je neman waɗanda suka ce a zo a yi nazari da su ba har bayan makonni da yawa. Ta yaya za mu tabbata cewa mun taimaki waɗannan mutanen kafin su daina sha’awar saƙonmu?—Mar. 4:14, 15.

Idan mutumin da ke son saƙonmu ba ya zama a yankinku, ku cika fom ɗin Please Follow Up (S-43) nan da nan kuma ku ba sakatare a taron ikilisiyarku na gaba. Sakataren ya ba da bayanin mutumin ga ikilisiyar da ke yankinsa ko kuma ya shigar da bayanin a sashen Congregation a dandalin jw.org sa’an nan ya aika zuwa ofishin reshe. Ya kamata ya yi hakan cikin kwana ɗaya ko biyu. Dattawa su riƙa shiga dandalinmu a kai a kai kuma idan aka sanar da su cewa su ziyarci wani, su ɗauki mataki nan da nan. Duk mai shela da aka tura ya je ya sami mutumin ya ɗauki wannan hakkin da muhimmanci sosai. Idan ba ku sami mutumin a gida ba, za ku iya rubuta sunanku da adireshinku ko kuma lambar wayarku kuma ku ajiye masa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba