Agusta Zai Zama Muhimmin Wata Cike da Ayyuka!
Za A Rarraba Wata Sabuwar Warƙa a Faɗin Duniya
1. Yayin da ake dab da cika shekara 100 da kafa Mulkin Allah, wane kamfen na musamman ne za mu yi a faɗin duniya?
1 Yayin da ake dab da cika shekara 100 da kafa Mulkin Allah, zai dace mu ɗaukaka Jehobah ta wajen yin wani kamfen na musamman. A watan Agusta, Shaidun Jehobah a faɗin duniya za su shagala da rarraba wata sabuwar warƙa mai jigo A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi? A cikin wannan warƙar an ƙarfafa mutane su nemi waɗannan amsoshin a cikin Littafi Mai Tsarki kuma an bayyana yadda dandalin jw.org zai taimake su su yi hakan.
2. Ta yaya mu ma za mu ‘yabi Ubangiji . . . da murya mai-ƙarfi’ a watan Agusta?
2 Yabo da Murya Mai Ƙarfi: Domin a taimaka wa masu shela su faɗaɗa hidimarsu, an ba waɗanda suke so su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Agusta damar yin awoyi 30 idan suna so. Tun da yake watan Agusta yana da Jumma’a biyar da Asabar biyar da kuma Lahadi biyar, masu shela ma’aikata za su sami zarafin yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Ƙari ga haka, matasa da suke hutun makaranta a watan Agusta za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Idan kana da ɗa ko kuma ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ke samun ci gaba kuma zai so ya zama mai shela, ka gaya wa mai tsara ayyukan rukunin dattawa nan da nan. Babu shakka, waɗannan da suka zama masu shela a wannan muhimmin watan za su sami ƙarfafa sosai. Majagaba na kullum da yawa a wasu ƙasashe sukan je hutu bayan sun cika awoyinsu na shekara, amma idan zai yiwu, zai dace su tsara ayyukansu don su yi wannan kamfen na musamman. Yanzu ne ya kamata iyalai su tattauna yadda za su tsara ayyukansu don su ma su ‘yabi Ubangiji . . . da murya mai-ƙarfi’ a watan Agusta.—Ezra 3:11; Mis. 15:22.
3. Me muke sa rai cewa za mu cim ma a wannan kamfen na musamman?
3 Ko da yake mun saba yin kamfen, muna fata wannan zai zama mafi girma a tarihi. Shin za mu sami sabon ƙoli a yawan awoyi da yawan masu shela da kuma yawan majagaba na ɗan lokaci a watan Agusta? Yayin da muke kammala shekarar hidima ta 2014, addu’armu ita ce Jehobah ya albarkaci mutanensa a faɗin duniya don ƙoƙarin da suke yi saboda watan Agusta ya zama wata mafi girma na yin wa’azi!—Mat. 24:14.