Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/14 p. 3
  • Tambayoyin Masu Shela

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyin Masu Shela
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Yi Amfani da Dandalinmu Wajen Koyar da Yaranku
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 5/14 p. 3

Tambayoyin Masu Shela

◼ Me ya wajaba yara su koya don su manyanta a dangantakarsu da Allah?

Iyaye Kiristoci suna iyakacin ƙoƙarinsu don su yi rainon ’ya’yansu “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Alal misali, iyaye suna tattauna nassosi tare da yaransu kowace safiya, kuma suna ganin amfaninsa. A lokacin ibada ta iyali ko kuma a wasu lokatai dabam, iyalai sukan kalli wani bidiyo tare, su tattauna wani batu daga jerin talifofin da ke sashen Young People Ask, su yi kwaikwayon wani labari daga Littafi Mai Tsarki ko kuma su yi gwaji a kan yadda za su bi wata shawara. Amma domin yara su ci gaba da “manyanta,” wajibi ne mu koya musu koyarwar Littafi Mai Tsarki masu zurfi.—Ibran. 6:1, New World Translation.

Ka yi la’akari da abubuwan da muke koya wa ɗalibanmu. A farkon haɗuwarmu da su ko kuma sa’ad da muka koma ziyara, muna ƙoƙarin soma nazari da su daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, wanda ya taimaka musu su san takamammun koyarwar Littafi Mai Tsarki. Bayan mun kammala wannan littafin, sai muka yi amfani da littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” wanda ya koya musu yadda za su bi mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwarsu. Yin nazarin waɗannan littattafan yana taimaka wa waɗanda suke koyon gaskiya su zama “dasassu” cikin Kristi da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya.’ (Kol. 2:6, 7) Shin waɗannan littattafan za su amfani yaranmu kuwa? Hakika. Yaranmu ma suna bukata a koyar da su game da fansa da Mulkin Allah da kuma yanayin matattu. Suna bukata su san dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mutane su sha wahala da kuma abubuwan da suka nuna cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe. Wajibi ne su kasance da tabbaci cewa Shaidun Jehobah ne suke koyar da gaskiya. Ƙari ga haka, ya kamata su fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za su iya horar da “hankulansu.” (Ibran. 5:14) Babu shakka, zai dace iyaye su lura da shekaru da kuma iyawar yaransu. Amma ƙananan yara da yawa suna iya fahimtar koyarwa masu zurfi daga Littafi Mai Tsarki tun suna ƙanana.—Luk 2:42, 46, 47.

Za a saka jerin talifofi da aka ɗauko daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a dandalin jw.org don a taimaka wa iyaye wajen yin nazari da yaransu. Iyalai za su iya samun waɗannan talifofin a ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA a dandalinmu. A nan gaba za a ci gaba da saka sababbin talifofi da aka ɗauko daga littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.” Amma iyaye za su iya yin amfani da waɗannan littattafai da aka buga. Iyaye ne za su tsai da shawara ko za su yi amfani da wannan littafin sa’ad da suke yin ibada ta iyali da yamma, sa’ad da suke nazari da kowane yaro ko kuma sa’ad da suke koya wa yaro yadda zai iya yin nazari da kansa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba