Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Hanyar Shirya Gabatarwarmu
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Idan gabatarwarmu ba ta da ban sha’awa, maigidan zai iya katse mana magana tun kafin mu idar da saƙonmu. Saboda haka, masu shela da yawa sun san cewa kalmomi na farko da suke furtawa su ne mafi muhimmanci a tattaunawarsu. Ko da yake akan rubuta gabatarwa dabam-dabam a cikin Hidimarmu ta Mulki da kuma Yadda Za a Soma Kuma Cigaba da Mahawwarai na Littafi Mai Tsarki, ba a rubuta cikakken gabatarwa domin ana so mutum ya yi amfani da nasa kalmomi. Ko da an rubuta cikakken gabatarwa ma, masu shela za su iya daidaita gabatarwar bisa ga nasu kalmomi. Saboda haka, shirya kalmomin da za mu faɗa da farko, maimakon faɗin duk abin da ya zo zuciyarmu zai taimaka mana mu ƙware a yin wa’azi.—Mis. 15:28.
Ku Bi Wannan Shawarar a Watan Nan:
Sa’ad da kuke ibada ta iyali, ku keɓe lokaci don shirya da kuma gwada yin amfani da gabatarwarku.
Sa’ad da kuka fita wa’azi, ku gaya wa abokin wa’azinku gabatarwa da kuka shirya. (Mis. 27:17) Ku canja gabatarwar idan ba ta shiga ba.