Tsarin Ayyuka na Makon 28 ga Afrilu
MAKON 28 GA AFRILU
Waƙa ta 35 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 6 sakin layi na 9-15 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Fitowa 19-22 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
Taron Hidima:
Waƙa ta 113
Minti 5: Ku Soma Nazari da Mutane a Ranar Asabar ta Farko. Jawabi. Ka ambata tsarin da aka yi don yin wa’azi a ranar Asabar ta farko a watan Mayu, kuma ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su fita wa’azi a ranar. Ka sa a yi gajeren gwaji da zai nuna yadda za a yi amfani da gabatarwa da ke shafi na 8.
Minti 15: “Sabon Tsari da Aka Yi ma Sababbin Warƙoƙi!” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sa a yi gwaji sau biyu. A gwaji na farko, a nuna yadda za a ba da sababbin warƙoƙin sa’ad da ake wa’azi gida-gida, sa’an nan a na biyun, a nuna yadda ake amfani da warƙoƙin sa’ad da aka koma a ziyarci wani mai sha’awar saƙonmu.
Minti 10: “Sabon Bidiyo don Soma Nazari da Mutane.” Jawabi. Ka saka bidiyon ko kuma ka kunna sautinsa don masu sauraro su kalla ko su ji, sai ka ba su dama su faɗi hanyoyi dabam-dabam da za a iya amfani da wannan bidiyon.
Waƙa ta 75 da Addu’a