Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/14 pp. 2-3
  • ‘Ka Tattara Dukan Jama’a’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Tattara Dukan Jama’a’
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Saurara don Ku Koya
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Tarurrukan Gunduma—Lokacin Yin Bauta da Farin Ciki
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 4/14 pp. 2-3

‘Ka Tattara Dukan Jama’a’

1. A wace hanya ce taron yanki da taron ƙasashe suka zo ɗaya da gagarumin taron da Isra’ilawa suka yi jim kaɗan da barin Masar?

1 Jim kaɗan bayan Isra’ilawa suka bar Masar, Jehobah ya umurci Musa ya ‘tattara dukan jama’a’ a Dutsen Sinai don su saurari kalmominsa, su ji tsoronsa kuma su koyar da ’ya’yansu don su bi dokokinsa. (K. Sha 4:10-13) Hakika, wannan taron ya ƙarfafa Isra’ilawa sosai kuma ba su manta da hakan ba. A cikin ’yan watanni masu zuwa, mutanen Jehobah za su yi taron yanki da kuma taron ƙasashe don su ji umurnin Jehobah. Me ya wajaba mu yi don mu amfana sosai?

2. Mene ne ya wajaba mu yi don mu nuna cewa mun “yi shiri”?

2 Ku “Yi Shiri”: Jehobah ya umurci dukan Isra’ilawa su “yi shiri” don wannan gagarumin taro a Dutsen Sinai. (Fit. 19:10, 11) Hakazalika, ba waɗanda suke da jawabi ko wani aiki a manyan taro ne kaɗai za su yi shiri ba, amma zai dace dukan waɗanda za su halarta su yi hakan. Alal misali, ’yan’uwa da yawa za su shirya don su ɗauki hutu daga aikinsu. Mai yiwuwa yanayinka ya zo ɗaya da na Nehemiya, mai ba wa Sarki Artaxerxes giya, wanda ya so ya ɗauki hutu daga aikinsa don ya koma Urushalima ya je ya sake gina ganuwarta. Amma ya san cewa sarkin zai iya ƙi da roƙonsa. Nehemiya ya yi addu’a kuma ya roƙi sarkin da gaba gaɗi da kuma kalmomi masu daɗi. Sai sarkin ya ba wa Nehemiya damar yin tafiyar, har ma ya tallafa masa da kayan aiki! (Neh. 2:1-9) Ƙari ga neman hutu daga shugabanka, ka shirya yadda za ka yi tafiyar da kuma inda za ka sauka? Dattawa za su yi farin cikin taimaka wa duk ɗan’uwan da yake bukatar taimako. Ka shirya yadda za ka halarci taron a kan lokaci kuma ka ƙudura cewa za ka “mai da hankali” sosai ga duk abin da za a faɗa a wurin.—Ibran. 2:1.

3. Mene ne zai taimaka mana mu shirya zukatanmu don taron?

3 Za mu kuma nuna cewa muna shirye ta wajen shirya zuciyarmu domin mu saurara kuma mu koya. (Ezra 7:10) An saka tsarin ayyuka na taron a dandalin jw.org kuma yana ɗauke da jigon dukan jawaban da za a bayar tare da nassi ɗaya ko biyu. Da haka, iyalai za su iya tsara abin da za su tattauna a Ibada ta Iyali da yamma zuwa lokacin taron. Wasu masu shela suna gurza tsarin ayyukan daga dandalinmu don su samu su rubuta muhimman batutuwan da mai jawabin yake faɗi.

4. Ta yaya iyaye za su yi amfani da waɗannan taron su koyar da ’ya’yansu?

4 Ku ‘Koya ma ’Ya’yanku’: Ɗaya daga cikin manufofin taron da aka yi a Dutsen Sinai ita ce, iyaye Isra’ilawa su “koya ma ’ya’yansu.” (K. Sha 4:10) Waɗannan taron suna ba iyaye damar koyar da ’ya’yansu su ma. Zai dace iyaye su zauna tare da yaransu sa’ad da ake ba da jawabai domin su taimaka musu su saurara. A ƙarshen kowace ranar taro da kuma sa’ad da suke ibada ta iyali, zai dace iyalai su tattauna abin da aka faɗa a taron.

5. Ta yaya za mu amfana daga halartan babban taron da ke tafe?

5 Gagarumin taron da aka yi a Dutsen Sinai ya taimaka wa Isra’ilawa su fahimci cewa zama mutanen Allah babban gata ne. (K. Sha 4:7, 8) Babban taron da ke zuwa ma zai amfane mu a wannan hanyar. A waɗannan kwanaki ukun, za mu kasance a wurin da babu mummunan tasirin duniyar Shaiɗan, za mu sami ƙarfafa kuma za mu more tarayya mai daɗi da ’yan’uwanmu. (Isha. 35:7-9) Yayin da ranar Jehobah take kusatowa, bari mu ƙudura cewa ba za mu fasa halartan wannan taro na shekara-shekara da zai ba mu damar ƙarfafa juna ba!—Ibran. 10:24, 25.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba