Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/13 pp. 1-5
  • Ku Saurara don Ku Koya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Saurara don Ku Koya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ka Tattara Dukan Jama’a’
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 8/13 pp. 1-5

Ku Saurara don Ku Koya

1. Me ya sa muke bukata mu dāge sosai don mu saurari abin da ake faɗa kuma mu koyi darussa masu kyau?

1 Ba da daɗewa ba za a soma taron gunduma na shekara ta 2013. An riga an yi nisa da shirye-shiryen abubuwan da za a gudanar a taron don ’yan’uwa a faɗin duniya su sami ƙarfafa. Kun shirya don ku halarci taron a duk ranaku uku da za a gudanar da shi? Akwai abubuwa da yawa da za su iya raba mana hankali a manyan taron gunduma, saboda haka, zai dace mu ƙoƙarta sosai don mu mai da hankali sa’ad da ake gudanar da taron. Tun da kowane sashe yana ɗaukan lokaci fiye da lokacin da muke yi a taron ikilisiya, muna bukata mu dāge sosai don mu mai da hankali a wannan lokaci. Ƙari ga haka, yin dogon tafiya da wasu abubuwa za su iya sa mu gajiya. Mene ne zai taimaka mana mu kasance a faɗake don mu saurari abin da ake faɗa kuma mu koyi darussa masu kyau?—K. Sh 31:12.

2. Ta yaya za mu shirya zukatanmu don taron gundumar?

2 Kafin a Soma Taron: An saka tsarin ayyuka da ke ɗauke da jigon jawaban da kuma ayoyi da ke bayyana darussan da za mu koya daga taron a dandalin www.jw.org. Idan za mu iya shiga wannan dandalin, zai dace mu karanta waɗannan bayanan don mu shirya zukatanmu don abubuwan da za a tattauna a taron. (Ezra 7:10) Sa’ad da kuke yin Bauta ta Iyali da yamma, zai dace ku yi nazarin wasu abubuwan da za a tattauna a taron don kowa a cikin iyalin ya riƙa marmarin taron.

3. Mene ne zai taimaka mana mu saurara sosai?

3 A Lokacin da Ake Taron: Idan zai yiwu, mu je ban-ɗaki kafin a soma taron. Ku kashe wayarku domin kada ta raba muku hankali sa’ad da aka kira da kuma aika muku saƙo, ko kuma ku yi tunanin aika saƙo a lokacin da ake gudanar da taron. Idan ya zama dole ku bar wayarku a kunne, zai dace ku saita ta yadda ba za ta dame mutane ba sa’ad da wani ya kira ku a waya. Idan kuna amfani da wata na’ura mai suna tablet, ku yi hakan a hanyar da ba za ta raba hankalin mutane sa’ad da ake taron ba. Kada ku yi ciye-ciye sa’ad da ake jawabi sai dai in da wata larura. (M. Wa. 3:1) Ku riƙa kallon mai jawabin. Idan ana karanta wata aya ku bi karatun ta wurin buɗe naku Littafi Mai Tsarki. Ku rubuta muhimman darussa da kuka koya.

4. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su saurara don su koyi muhimman darussa a taron?

4 Ƙari ga haka, muna son yaranmu su saurari abin da ake faɗa a taron don su koyi muhimman darussa. Misalai 29:15 ta ce: “Yaro wanda an ƙyale shi za ya jawo wa uwatasa kunya.” Saboda haka, ya kamata iyaye su zauna tare da yaransu don su tabbata cewa yaran suna sauraron abin da ake faɗa a taron maimakon yin surutu ko yawo ko kuma aika saƙon tes. Ko da yaran ƙanana ne kuma ba sa fahimtar dukan abubuwan da ake faɗa, zai dace a horar da su don su iya zama shiru suna sauraro ba tare da barci ba.

5. Me ya sa yake da amfani mu yi bitar abubuwan da muka koya a taron, kuma ta yaya za mu yi hakan?

5 Bayan An Gama Taro Kowace Rana: Kada ku yi dare a waje. Ku riƙa barci da wuri don ku huta da kyau. Idan kun yi bitar abin da aka faɗa a wurin taron, ba za ku mance su da sauri ba. Saboda haka, zai dace iyalai su ɗauki ’yan mintoci da yamma don su tattauna abin da suka koya a taron. Idan kuka je gidan cin abinci da abokai, zai dace ku je da abin da kuka rubuta don ku tattauna wasu abubuwa a ciki. Bayan kun koma gida, kuna iya tattauna yadda za ku yi amfani da wannan bayanan a matsayin iyali sa’ad da kuke Bauta ta Iyali da yamma. Ƙari ga haka, za ku iya keɓe lokaci kowane mako don karanta sababbin littattafai da aka fitar.

6. Shin kasancewa a wurin taron ne kawai ake bukata a gare mu? Ka bayyana.

6 Idan ba a ci abinci an ƙoshi a wajen biki ba, to bikin bai yi ba. Haka yake da koyarwar da muke samu a taron gunduma. Bari mu yi ƙoƙari mu halarci dukan sassan taron kuma mu mai da hankali sosai don mu saurari abubuwan da za a gudanar da kuma yi amfani da abin da muka koya.

[Akwati a shafi na 4]

Tunasarwa Game da Taron Gunduma na Shekara ta 2013

◼ Lokatan Taro: Za a soma taron ne da ƙarfe 9:20 na safe a dukan kwanaki uku. Sa’ad da aka gabatar da kaɗe-kaɗe, ya kamata dukanmu mu zauna don a soma taron da tsari. Za a gabatar da waƙa da kuma addu’ar kammala taron da ƙarfe 4:50 na yamma a ranar Juma’a da Asabar, kuma da ƙarfe 3:35 na yamma a ranar Lahadi.

◼ Ajiye Mota: A dukan wuraren taron gunduma, ’yan atenda za su nuna wa mutane inda za su ajiye motocinsu kyauta, waɗanda suka fara zuwa ne za a fara ba su wajen ajiye mota. Don Allah ku ba su haɗin kai.—1 Kor. 13:4, 5.

◼ Kama Wajen Zama: Za ku iya kama wajen zama wa waɗanda kuke tafiya tare a cikin motarku ko waɗanda kuke zama tare a gida ɗaya, ko kuma waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su a yanzu kawai.—1 Kor. 13:5.

◼ Abincin Rana: Don Allah ku kawo abincin da za ku ci da rana, maimakon ku fita waje don sayan abinci a lokacin shan iska. Za ku iya yin amfani da ƙaramin koola da za ku iya ajiyewa a ƙarƙashin kujera. Ba a yarda a kawo babbar koola da kuma tambulan a wajen taron gundumar ba.

◼ Ba da Kyauta: Za mu iya nuna godiya ga shirye-shiryen da aka yi don gudanar da taron ta wajen ba da kyauta da son rai a wajen taron gundumar. Hakan zai taimaka wajen tallafa wa aikin wa’azi da ake yi a dukan duniya. Idan za ku ba da gudummawa ta hanyar cek a wurin taron, ku rubuta kalmomin nan biyu, “Watch Tower” a kan cek ɗin. Ƙari ga haka, za ku iya ba da gudummawarku ta ATM.

◼ Haɗari da Jinyar Gaggawa: Idan wani yana bukatar jinyar gaggawa a wurin taro, don Allah ku sanar da ɗan atenda da ke kusa, wanda zai kai marar lafiyar zuwa Sashen Kula da Jinyar Gaggawa domin ƙwararrun ma’aikatan jinya su duba abin da yake damunsa kuma su ba da taimako.

◼ Magunguna: Idan kuna da wani maganin da kuke sha a kai a kai saboda rashin lafiya, don Allah ku taho da shi, tun da ba za a tanadar da shi a wurin taron gundumar ba. Idan kuna karɓan allura saboda ciwon sukari, ya kamata ku zubar da allurar da kuma sirinjin a inda ya dace. Kada ku zuba a kwandon sharar da ke wurin taron gundumar ko kuma a inda kuka sauka.

◼ Takalma: Kowace shekara ana samun rauni sakamakon irin takalma da ake sakawa, musamman masu tsini. Saboda haka, ya kamata a saka takalma da za a ji daɗin tafiya da su kuma waɗanda ba su da tsini sosai.

◼ Keken Jarirai da Kujerun Shaƙatawa: Kada a kawo keken jarirai da kujerun shaƙatawa zuwa wurin taron. Amma dai, za ku iya zuwa da kujerun yara mai kāriya idan za a sa yaran su zauna a kai kusa da iyayensu.

◼ Turare: Saboda waɗanda ke fama da ciwon ƙirji ko makamancin haka, ya kamata mu rage yadda muke amfani da turare masu ƙanshi sosai a taron gundumar, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu.—1 Kor. 10:24.

◼ Fom Ɗin Please Follow Up (S-43): Ku yi amfani da fom ɗin Please Follow Up (S-43) don ba da bayani game da wani da yake son saƙonmu da kuka haɗu da shi sa’ad da kuke wa’azi a lokacin taron. Za ku iya kai fom ɗin zuwa Sashen Kula da Littattafai ko kuma ku ba sakataren ikilisiyarku sa’ad da kuka koma gida.

◼ Gidan Abinci da Masu Sayar da Abubuwa a Waje: Ku girmama sunan Jehobah ta nuna hali mai kyau a gidajen abinci. Ku saka tufafi da zai nuna cewa ku Kiristoci na gaskiya ne. Ba zai dace mu riƙa zuwa sayan abubuwa a lokacin da ake taron ba.

◼ Masauki:

(1) Don Allah kada ku kama ɗakuna fiye da waɗanda kuke bukata kuma kada mutanen da suke kwana a ɗakin da kuka kama su wuce adadin da aka umurta.

(2) Kada ku bar ɗakin da aka ba ku ba gaira ba dalili amma idan wata bukatar gaggawa ta taso, ku sanar da ma’aikatan hotal ɗin ba tare da ɓata lokaci ba don a ba da ɗakin ga wasu da suke bukata. (Mat. 5:37) Idan ba ku bar ɗakin kwana biyu kafin nan ba, wataƙila ba za a mayar muku da kuɗinku ba.

(3) Idan kuka ɗauki wani abu da aka tanadar a masaukinku don yin amfani da shi, ku mayar da zarar kun gama aiki da shi don wasu su samu su yi amfani da shi.

(4) Za ku iya ba da kyauta wa masu aiki a hotal ɗin ko wasu da suka taimaka da ɗauka muku kaya.

(5) Ku yi dahuwa a wuraren da aka amince da yin hakan ne kawai. Kada ku yi dahuwa a lokacin da ake yin taro domin hakan ba zai nuna cewa muna girmama Allah ba.

(6) Idan ana tanadar da abincin safe a inda kuka sauka, ku ɗauki daidai abincin da aka ajiye muku kawai.

(7) Ku bar halinku ya nuna cewa kuna da ruhu mai tsarki sa’ad da kuke sha’ani da ma’aikatan hotal da kuma ’yan’uwa da ke Sashen Kula da Ɗakuna. Suna kula da mutane da yawa kuma saboda haka, idan muka nuna alheri, haƙuri da kuma sanin yakamata, za mu sa su yi aikinsu da kyau.

(8) Iyaye su riƙa kula da yaransu a kowane lokaci sa’ad da suke inda suka sauka, ko a hotal ko a wani wuri dabam.

(9) Kada ku zauna a ɗakunan da ’yan Kula da Sashen Ɗakuna ba su ba ku ba. Ku ba da haɗin kai ta wajen sauka a inda aka kama muku. Kada ku yi dare a waje. Idan kai namiji ne, kada ka kwana a ɗakin da aka keɓe wa mata, mace kuma kada ta kwana a inda aka keɓe wa maza.

(10) Idan kuka sami matsala a inda kuka sauka, ku je ku sanar da Sashen Kula da Ɗakuna sa’ad da kuke wurin taron don ku sami taimako.

◼ Ba da Kai don Yin Hidima: Ya kamata duk wanda yake son ya ba da kai ya je Sashen Kula da Hidima a wurin taron gundumar. Yara da ba su kai shekara sha shida ba tukun za su iya ba da kansu ta yin aiki tare da iyayensu ko kuma da wani da ya manyanta, wanda iyayen suka amince da shi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba