Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/14 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 1/14 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Fabrairu

“Mutane da yawa suna ɗokin ganin dawowar Yesu. Mene ne kake ganin manufar dawowar Yesu?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa bangon baya na Hasumiyar Tsaro ta Janairu–Fabrairu, sa’an nan ku tattauna abin da ke ƙarƙashin tambaya ta farko, da kuma aƙalla nassi ɗaya a cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna tambaya da ke gaba.

Hasumiyar Tsaro Janairu–Fabrairu

“Mutane da yawa suna tunani a kan wannan tambayar: ‘Idan Allah yana ƙaunarmu, me ya sa yake ƙyale mu mu sha wahala haka?’ Ka taɓa irin wannan tunanin? [Ka bari ya ba da amsa.] Bari in nuna maka abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da abin da zai faru da ’yan Adam a nan gaba. [Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:5.] Talifin da ke shafi na 13 a cikin wannan mujallar ya nuna yadda Allah zai cika wannan alkawarin.”

Awake! Fabrairu

“Muna ziyartar mutane ne don mu yi magana da su a kan wani abu da kusan kowa yana fama da shi, wato, rashin isashen lokaci. Kamar dai ba zai yiwu mu sami lokacin yin dukan abubuwa da muke so mu yi ba. Kana ganin abubuwan yi ne suka yi mana yawa ko dai muna ɓata lokaci sosai a yin abubuwa da ba su da muhimmanci? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa ba su san cewa Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarwari da za su taimaka mana mu yi amfani da lokacinmu a hanyar da ta dace ba. Ga wani misali. [Karanta Filibiyawa 1:10a.] Wannan mujallar ta bayyana abubuwa huɗu da suka taimaka wa mutane da yawa su yi amfani da lokacinsu da kyau.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba