Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/13 p. 8
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Yadda Za a Gabatar
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 12/13 p. 8

Gabatarwa

Bisharar Mulki ta 38

“Muna kamfen ne a duk faɗin duniya don mu rarraba wannan warƙa da ke ɗauke da saƙo mai muhimmanci. Ga naka.”

Abin lura: Zai dace ku gajerta maganarku, domin ku iya rarraba warƙar a dukan yankinku. Amma, a wasu lokatai za ku iya samun mutane da ke son saƙonmu sosai kuma za su so ku tattauna da su. A wannan yanayin, za ku iya ku tambayi ra’ayinsa game da tambayar da ke bangon gaba na warƙar, sa’an nan ku karanta amsar da ke cikin warƙar, wadda aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki, kuma ku ɗan tattauna wasu bayyanai a cikin warƙar idan da hali. Kafin ku tafi, ku nuna masa tambayar da ke ƙarƙashin sashen nan “Ka Yi Tunani a Kan Wannan Tambayar” kuma ku gaya masa cewa za ku dawo don ku tattauna ta.

Hasumiyar Tsaro Janairu–Fabrairu

“A yau, da ƙyar mutane suke samun lokacin yin tunani game da Allah, domin sun shagala da harkoki dabam-dabam. Kana ganin zai dace mu ɗauki Allah da muhimmanci a rayuwarmu? [Ka bari ya ba da amsa.] A lokacin da Yesu yake duniya, ya ambata cewa muna bukatar ƙulla dangantaka mai kyau da Allah idan muna so mu kasance da farin ciki sosai. [Karanta Matta 5:3.] Wannan mujallar ta tattauna dalilai uku da suka sa muna bukatar Allah a rayuwarmu.”

Awake! Janairu

“Za ka yarda cewa iyalai da yawa suna fuskantar matsaloli da dama a yau, ko ba haka ba? [Ka bari ya ba da amsa.] Akwai wani ƙarin magana a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna mana abin da ya wajaba iyalai su yi don su kyautata zamansu a matsayin iyali. [Karanta Misalai 24:3.] Mutane da yawa sun gano cewa bin shawarar Littafi Mai Tsarki tafarki mai hikima ne sosai. Wannan mujallar ta tattauna wani Dandali na musamman da ake samun bayanai daga Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa iyalai.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba