Sanarwa
◼ Littattafan da za a ba mutane a watan Disamba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, Za Ka So Ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, ko kuma duk wata warƙa da kuke da ita a ikilisiyarku. Janairu: Kamfen na musamman don rarraba Bisharar Mulki ta 38, mai jigo Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? Idan aka gama rarraba Bisharar Mulki ta 38 kafin ƙarshen watan, sai a soma ba mutane littattafan da ya kamata a rarraba a watan gobe. Fabrairu: Albishiri Daga Allah!, Ka Saurari Allah, Ka Saurari Allah don Ka Rayu Har Abada, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same Ta Kuwa? ko kuma duk wata ƙasida mai shafuffuka 32 da kuke da ita a ikilisiyarku. Don Musulmai: Cikakken Imani—Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa, Shiriyar Allah—Hanyarmu ta Samun Aljanna ko kuma su biyun a take. Maris: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake!
◼ Za a yi taron Tuna mutuwar Yesu na shekara ta 2015 a ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2015.