Za A Soma Nazarin Littafin Nan Ka Kusaci Jehovah a Makon 6 ga Janairu
1. Somawa da makon 6 ga Janairu, mene ne za a yi da zai taimaka mana mu ƙara kusantar Jehobah?
1 Jehobah yana so mu kusace shi. (Yaƙ. 4:8) Somawa da makon 6 ga Janairu, za mu yi nazarin littafin nan Ka Kusaci Jehovah a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Hakan zai taimaka mana mu kusaci Jehobah. An bayyana manufar wannan littafin a shafinsa na farko cewa: “Bimbini bisa hanyar da Jehovah yake nuna kowanne cikin halayensa, ganin yadda Yesu Kristi ya nuna su, da kuma fahimtar yadda mu ma za mu iya koyonsu za su sa mu kusaci Allah.” Ikilisiyoyin Hausa sun yi nazarin wannan littafin a shekara ta 2011 zuwa 2013. Saboda haka, ’yan’uwa da yawa da ba su taɓa yin nazarinsa ba za su sami damar koyan halayen Jehobah dalla-dalla ta wannan nazarin. Waɗanda sun riga sun yi nazarin littafin nan ma za su amfana domin sake yin nazarin zai taimaka musu su daɗa fahimtar halayen Jehobah.—2 Bit. 1:12.
2. Yaya za a yi nazarin littafin nan Ka Kusaci Jehovah?
2 Yadda Za A Yi Nazarin Littafin: Mai gudanar da nazarin zai soma da ɗan gabatarwa, wataƙila furuci ɗaya ko biyu. Ba a ƙayyade nassosin da ya kamata a karanta a cikin wannan littafin ba. Saboda haka, mai gudanar da nazarin ne zai zaɓi muhimman nassosi da za a karanta. A ƙarshen kowane darasi, zai iya yin amfani da tambaya ɗaya ko biyu don bita. Idan akwai akwatin nan “Tambayoyi don Bimbini” a sashen da ake nazarinsa, sai a yi amfani da shi wajen yin bita. Idan da lokaci, mai gudanar da nazarin zai iya sa a karanta wasu cikin nassosin da ke akwatin, sa’an nan ya yi ƙarin tambayoyi da za su sa masu sauraro su yi kalami daga zuciyarsu.
3. Mene ne ya kamata mu yi yayin da ake nazarin littafin nan, kuma me ya sa?
3 Ku Amfana Sosai: Ku yi shiri da kyau kafin nazarin ko da kun taɓa yin nazarin littafin. Ku yi kalami sa’ad da ake nazarin, domin hakan zai sa ku yabi Jehobah, ku ƙarfafa waɗanda suka halarci taron, kuma ku riƙa tuna da abin aka yi nazarinsa. (Zab. 35:18; Ibran. 10:24, 25) Yayin da kuke yin bimbini a kan halayen Jehobah da babu kamarsu, za ku ƙara kusantarsa. (Zab. 77:11-13) A sakamakon haka, za ku ƙara dāgewa wajen bin dokokinsa da kuma yi wa mutane wa’azi game da shi.—Zab. 150:1-6.