Tsarin Ayyuka na Makon 16 ga Disamba
MAKON 16 GA DISAMBA
Waƙa ta 116 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 20-22 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ru’ya ta Yohanna 1-6 (minti 10)
Na 1: Ru’ya ta Yohanna 3:14–4:8 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Iblis Halitta Ne na Gaske?—td 22A (minti 5)
Na 3: A Wace Hanya Ce Yesu Ya Yi wa Almajiransa “Kwatanci”?—Yoh. 13:15 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 44
Minti 10: Yadda Za Mu Amfana Idan Muka Shirya Abin da Za Mu Faɗa Kafin Mu Fita Wa’azi. Ka tattauna bayanin da ke sakin layi na 1 a shafi na 167 zuwa sakin layi na 1 a shafi na 168 a cikin littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education. Sai ka sa wani ɗan’uwa ya nuna yadda yake amfani da littattafan da ya kamata mu ba mutane a watan wajen shirya abin da zai faɗa a wa’azi. Dan’uwan ya yi-wa-kansa-magana.
Minti 10: Ya Dace Matasa Su Yabi Jehobah. (Zab. 148:12, 13) Ka gana da matasa biyu ko uku da suke da hali mai kyau. Waɗanne ƙalubale game da imaninsu ne suke fuskanta a makaranta? Ta yaya iyayensu da kuma sauran ’yan’uwa suka taimaka musu su sha kan waɗannan ƙalubalen? Mene ne ya taimaka musu su bayyana imaninsu da gaba gaɗi? Ka ba su dama su ba da labarin abin da ya faru da su a makaranta.
Minti 10: “Za A Soma Nazarin Littafin Nan Ka Kusaci Jehovah a Makon 6 ga Janairu.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 75 da Addu’a