Tsarin Ayyuka na Makon 9 ga Satumba
MAKON 9 GA SATUMBA
Waƙa ta 62 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 14 sakin layi na 1-9 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Korintiyawa 10-16 (minti 10)
Na 1: 1 Korintiyawa 14:7-25 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ta Yaya Mutum da Ya Yi Zunubi Zai “Roƙi Ubangiji”?—2 Laba. 33:12, 13; Isha. 55:6, 7 (minti 5)
Na 3: An Rubuta Littafi Mai Tsarki don Mutane a Dukan Ƙasashe da Al’adu—td 30C (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 89
Minti 10: Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?—Sashe na 1. Jawabi bisa ga bayanin da ke sakin layi na 1-9 a warƙar nan Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? Ka yaba wa matasa da suke saka al’amura na mulkin Allah farko a rayuwarsu.
Minti 10: Labaran Abubuwa da Suka Faru Sa’ad da Aka Yi Amfani da Ƙasidar Albishiri Daga Allah! Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su ba da labaran abubuwan da suka faru sa’ad da suka yi amfani da ƙasidar Albishiri Daga Allah! wajen soma nazari da mutane. Ka sa a yi gwajin da zai nuna yadda za a iya yin amfani da ƙasidar sa’ad da aka koma don a ziyarci wani da ya karɓi mujallunmu.—Ka duba Hidimarmu ta Mulki na Maris 2013, shafi na 7.
Minti 10: “Ku Bi Gurbin Annabawa—Amos.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 96 da Addu’a