Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Satumba
“Kusan kowa yakan yi addu’a a wani lokaci. Har waɗanda ba su gaskata cewa akwai Allah ba suna yin addu’a sa’ad da suka shiga matsala. Shin kana ganin Allah yana jin dukan addu’o’i ne?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa bangon bayan Hasumiyar Tsaro ta Satumba–Oktoba kuma ku tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta farko. Ka karanta aƙalla ɗaya cikin Nassosin da aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallar kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na biyu.
Hasumiyar Tsaro Satumba–Oktoba
“Shin ka taɓa ji kamar ana bukatar canji a duniya bayan ka lura da abubuwan da suke faruwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka yi la’akari da misali mai kyau da mahaliccinmu ya kafa a kan yadda za mu daidaita ra’ayinmu game da adalci kuma mu kasance da ƙauna. [Karanta Zabura 103:8-10.] Sa’ad da kake karanta labarin da ke shafi na 10 a wannan mujallar, za ka ga yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu daina baƙin ciki ainun don rashin adalcin da ake yi a duniya.”
Awake! Satumba
“Mutane da yawa sun amince cewa jima’i tsakanin marasa aure zunubi ne. Amma idan suka yi abin da zai ta da sha’awa tsakaninsu ba tare da sun yi jima’i ba, ba su yi laifi ba. Mene ne ra’ayinka game da wannan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a nan. [Karanta Afisawa 5:3.] Talifin da ke shafi na 4 a cikin wannan mujallar ya tattauna ra’ayin Allah game da irin wannan halin da kuma yadda hakan ya shafe mu.”