Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/13 p. 7
  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 8/13 p. 7

Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 26 ga Agusta, 2013. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan ne domin ku yi bincike sa’ad da kuke shiri don makaranta a kowane mako.

1. Wane darasi ne za mu koya daga Sarki Hirudus a yadda ya yarda mutane su ba shi daraja da kuma yabo da ba su dace da shi ba? (A. M. 12:21-23) [1 ga Yuli, w08 5/15 shafi na 32, sakin layi na 7]

2. Wane amfani ne Kiristoci matasa za su iya more daga yin nazari a kan labarin Timotawus da kuma bin misalinsa? (A. M. 16:1, 2) [8 ga Yuli, w08 5/15 shafi na 32, sakin layi na 10]

3. Ta yaya Biriskilla da Akila suka taimaka wa Afolos bayan sun saurare shi sa’ad da yake yin ‘magana da gaba gaɗi’ a cikin majami’a a Afisus? (A. M. 18:24-26) [15 ga Yuli, w10 6/15 shafi na 11, sakin layi na 4]

4. Wane sadaukarwa ne manzo Bulus ya yi don bishara? (A. M. 22:3) [22 ga Yuli, w09 9/15 shafi na 24 sakin layi na 13]

5. Mene ne keɓe kai ga Allah yake nufi? (A. M. 27:22-24) [29 ga Yuli, w10 1/15 shafi na 3 sakin layi na 2]

6. Ta yaya mutane da yawa a yau suke nuna rashin daraja ga aure da kuma Jehobah Allah? (Rom. 1:24-32) [5 ga Agusta, w11 1/15 shafi na 13 sakin layi na 3]

7. Ta yaya “fansa da . . . Yesu Kristi” ya biya a shekara ta 33 a zamaninmu ta share ‘zunuban’ mutanen dā kafin a biya ta? (Rom. 3:24, 25) [5 ga Agusta, w08 6/15 shafi na 29, sakin layi na 6]

8. Wane tanadi ne Jehobah ya yi don ya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar wani yanayi mai tsanani sosai har ba mu san takamaiman abin da za mu ambata a addu’armu ba? (Rom. 8:26, 27) [12 ga Agusta, w08 6/15 shafi na 30 sakin layi na 10]

9. Mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ba da umurni cewa mu riƙa karɓan “baƙi”? (Rom. 12:13) [19 ga Agusta, w09 10/15 shafi na 5 sakin layi na 12-13]

10. Ta yaya za mu bi “halin Ubangiji Yesu Almasihu,” kamar yadda manzo Bulus ya shawarta? (Rom. 13:14) [26 ga Agusta, w05 1/1 shafuffuka na 23-24 sakin layi na 20-22]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba