Tsarin Ayyuka na Makon 19 ga Agusta
MAKON 19 GA AGUSTA
Waƙa ta 51 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 12, sakin layi na 10-16 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Romawa 9-12 (minti 10)
Na 1: Romawa 9:19-33 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Littafi Mai Tsarki Daga Allah Ne—td 30A (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Bai Kamata Mu Ji Tsoron ’Yan Adam Ba—Luk 12:4-12 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 113
Minti 5: “Yadda Za A Ba da Mujallu a . . .” Tattaunawa.
Minti 15: “Ku Yi Zaman Lafiya da Dukan Mutane.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sa a yi gajeren gwaji. Da farko, gwajin ya nuna abin da bai kamata mu yi ba sa’ad da wani yana fushi sosai don mun zo masa wa’azi. Daga baya kuma, gwajin ya nuna matakin da ya kamata mu ɗauka a irin wannan yanayi.
Minti 10: Ku Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi. (Ayyukan Manzanni 4:29) Ka tattauna abin da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2009, shafuffuka na 22-23, sakin layi na 15-17. Ka ba wa masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Waƙa ta 92 da Addu’a