Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/13 p. 6
  • “Yadda Za A Ba da Mujallu a . . .”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Yadda Za A Ba da Mujallu a . . .”
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 8/13 p. 6

“Yadda Za A Ba da Mujallu a . . .”

An saba gabatar da wani sashe a Taron Hidima a kan yadda za a ba da mujallu. Ba wai ana hakan don a yi bitar abubuwan da ke cikin mujallun ba ne, amma don tattauna yadda za a ba da mujallun ne. Saboda haka, ɗan’uwan da zai gudanar da wannan sashen zai bi umurnin da aka ba shi yayin da yake yin ’yar gajeriyar gabatarwa da za ta sa a so mujallun. Bayan haka, ya gaya wa masu sauraro da dama su faɗi yadda za su gabatar da wani talifi ko kuma jerin talifofi a cikin mujallar don wasu masu shela su san yadda su ma za su gabatar da mujallun. Maimakon ya gaya wa ’yan’uwa su faɗi dukan abubuwan da za su faɗa sa’ad da suke ba da mujallun, zai dace ya ba su damar faɗan tambayoyin za su yi da za su sa mutane a yankin su so mujallun, sa’an nan su faɗi nassin da za su karanta. Sai ya kammala ta wajen sa a gwada yadda za a ba da kowace mujalla. An ƙarfafa mu mu riƙa karanta waɗannan mujallun kafin mu zo taro kuma mu yi kalami a kan yadda za mu ba da su. Idan kowa ya shirya da kyau, wannan sashen zai taimaka wa ’yan’uwa duka su ƙware a yin wa’azi.—Mis. 27:17.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba