Babban Zarafi na Yabon Jehobah
1. Wane sabon tsari ne zai taimaka mana mu ‘yabi’ Jehobah sosai?
1 Somawa daga watan Maris da ya shige, an ƙaddamar da wani sabon tsari da zai ba wa masu shela damar ba da sa’o’i 30 a matsayin majagaba na ɗan lokaci a watannin Maris da Afrilu da kuma a watan da mai kula da da’ira yake ziyara. Idan ziyarar mai kula da da’ira ta soma a ƙarshen wata kuma ta shiga wani sabon wata, masu shela da suke so su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci na sa’o’i 30 za su zaɓi wata ɗaya a cikin biyun don yin hidimar. Waɗanda suke yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a wannan lokaci za su iya halartar taron da mai ziyara zai yi da majagaba na kullum da na musamman daga farko har ƙarshe. Wannan yana nufin cewa idan ba za mu iya yin hidima na sa’o’i 50 a wata ba, za mu iya ‘yabon’ Jehobah sosai ta yin hidima na sa’o’i 30 sau huɗu a shekara!—Zab. 109:30; 119:171.
2. Wane gata ne waɗanda za su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da mai kula da da’ira ya zo ikilisiyarsu za su mora?
2 Lokacin Ziyarar Mai Kula da Da’ira: Yanzu ’yan’uwa da yawa za su sami damar yin hidima na ɗan lokaci sa’ad da mai kula da da’ira ya ziyarci ikilisiyarsu, kuma za su sami ƙarfafa idan suka yi wa’azi tare da shi da matarsa. (Rom. 1:11, 12) Majagaba na ɗan lokaci da yawa za su iya ɗaukan hutun kwana ɗaya daga aiki don su yi wa’azi tare da mai ziyarar a mako. Wasu ’yan’uwa da suke aiki daga Litinin zuwa Jumma’a za su iya fita wa’azi tare da shi a ranar Asabar ko kuma Lahadi idan hakan zai yiwu. Ƙari ga haka, ’yan’uwa da suke hidima na ɗan lokaci za su sami ƙarfafa idan suka halarci taron da mai ziyara zai yi da majagaba na kullum da kuma na musamman, ko ba haka ba?
3. Me ya sa lokacin Tuna mutuwar Yesu dama ce mai kyau don yin hidimar majagaba na ɗan lokaci?
3 A Watannin Maris da Afrilu: Waɗanda a dā suka bi tsarin yin sa’o’i 30 a hidimar majagaba na ɗan lokaci na wata ɗaya a lokacin Tuna mutuwar Yesu za su iya ninka yadda suke ba Jehobah “hadaya ta yabo” sau biyu yanzu! (Ibran. 13:15) Watannin Maris da Afrilu watanni ne masu kyau da za su ba mu dama na ƙara ƙwazo a wa’azi a matsayin majagaba na ɗan lokaci. Kowace shekara a wannan lokacin, muna jin daɗin yin kamfen na gayyatar mutane zuwa taron tunawa da mutuwar Yesu. Ƙari ga haka, masu shela da yawa suna ƙara ƙwazo a wa’azi a lokacin tunawa da mutuwar Yesu, saboda haka za mu sami damar fita wa’azi da masu shela dabam-dabam. Bayan taron Tuna mutuwar Yesu, za mu ƙoƙarta mu sake ziyartar waɗanda suka halarci taron don mu sake gayyatar su zuwa jawabi na musamman da za a yi bayan taron Tuna mutuwar Yesu. Shin za ka so ka yi amfani da wannan dama na musamman don yin hidimar majagaba na ɗan lokaci?—Luk 6:45.