Tsarin Ayyuka na Makon 17 ga Yuni
MAKON 17 GA YUNI
Waƙa ta 48 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 8, sakin layi na 1-9 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayyukan Manzanni 5-7 (minti 10)
Na 1: Ayyukan Manzanni 5:17-32 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Ya Wajaba Mutum Ya Yi don Jehobah Ya San Shi?—2 Tim. 2:19 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Mukan Koma Mu Ziyarci Waɗanda Muka Yi Musu Wa’azi?—td 8B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 61
Minti 10: Yadda Za Mu Nuna Ladabi a Wa’azi. Jawabi a kan bayanin da ke shafi na 190, sakin layi na 1 zuwa shafi na 192, sakin layi na 1 a cikin littafin nan, Benefit From Theocratic Ministry School Education. Ka sa a ɗan nuna wani mai shela yana wa’azi amma ba ya nuna ladabi ga maigidan. A nuna ainihin abin da zai iya faruwa a yankinmu. Sa’an nan ka sa a sake maimaita gwajin, amma a wannan karon, mai shelar ya nuna ladabi yadda ya kamata.
Minti 10: Ku Taimaka Wa Ɗalibinku Ya Zama Mai Shela. Ka tattauna bayanin da ke shafi na 78, sakin layi na 3 zuwa bayani da ke ɗigo na ƙarshe a shafi na 80 a cikin littafin Organized to Do Jehovah’s Will.
Minti 10: “Babban Zarafi na Yabon Jehobah.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka ɗan gana da mai shela ɗaya ko biyu da suka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da mai kula da da’ira ya ziyarci ikilisiyarku.
Waƙa ta 9 da Addu’a