Tsarin Ayyuka na Makon 13 ga Mayu
MAKON 13 GA MAYU
Waƙa ta 4 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 5, sakin layi na 8-14 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Yohanna 5-7 (minti 10)
Na 1: Yohanna 6:22-40 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Wane Ne Ya Sa Muke Shan Wahala?—td 32A (minti 5)
Na 3: Wane Darasi Ne Za Mu Koya Daga Littafin Lissafi 15:37-40? (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 126
Minti 10: Littattafan da Za A Ba da a Watannin Mayu da Yuni. Jawabi. Ka ɗan bayyana dalilin da ya sa mutane a yankinku za su so warƙoƙin da za a ba da a wa’azi. Ka sa a yi gwaji ɗaya ko biyu a kan yadda za a ba da warƙoƙin sa’ad da ake wa’azi gida-gida.
Minti 10: Mene Ne Muka Koya? Tattaunawa. Ka sa a karanta Matta 5:11, 12 da Matta 11:16-19. Ka tattauna yadda waɗannan ayoyin za su iya taimaka mana a hidimarmu.
Minti 10: “Me Yake Motsa Mu Mu Yi Wa’azi?” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 91 da Addu’a