Sanarwa
◼ Littattafan da za a ba da a watan Afrilu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da kuke koma ziyara, ku gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun nan, Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada idan sun dace da mutumin, kuma ku yi ƙoƙarin soma nazari da mutumin. Mayu da Yuni: Ku yi amfani da warƙoƙin da kuke da su a ikilisiya. Idan kuka sami wanda yake son saƙonmu, ku nuna masa yadda muke amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada wajen nazari da mutane. Yuli: Albishiri Daga Allah! ko ɗaya daga cikin ƙasidun nan masu shafuffuka 32: Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada. Idan kana wa Musulmi wa’azi, za ka iya ba shi ƙasidar nan Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa ko kuma Shiriyar Allah—Hanyarmu ta Samun Aljanna.
◼ A duk lokacin da shirin tafiyarku zuwa wata ƙasa ya haɗa da halartar taron gunduma a ƙasar, za ku iya samun bayanai da za su taimaka muku a dandalinmu na www.jw.org idan kuka danna “Conventions” a sashen “About Us.”
◼ A ranar Jumma’a, 24 ga Mayu, 2013 ba za a bar baƙi su shiga Bethel ba. Saboda haka, don Allah kada ku zo karɓan littattafai ko kuma yawon buɗe ido a wannan ranar.