Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/13 p. 8
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Yadda Za a Gabatar
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 4/13 p. 8

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Mayu

“Muna ƙarfafa maƙwabtanmu su karanta Littafi Mai Tsarki. Amma mutane da yawa suna ganin kamar Littafi Mai Tsarki yana da wuyar fahimta. Shin mene ne ra’ayinka game da hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da aka faɗa a cikin mujallar nan.” Ka nuna masa talifin da ke bangon baya na Hasumiyar Tsaro na Mayu-Yuni 2013. Ku tattauna sakin layi na ɗaya da kuma aƙalla nassi ɗaya daga cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba mutumin mujallun, kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna tambaya da ke biye.

Hasumiyar Tsaro Mayu-Yuni

“Dukan mutanen da muka tattauna da su suna fama da matsaloli. Kuma hakan ya sa wasu suna tambaya ko rayuwa tana da ma’ana. A ganinka, mene ne yake hana mutane samun farin ciki a rayuwa yau? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa ba da daɗewa ba, Allah zai kawar da matsalolin da muke fuskanta a yau. [Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 21:4.] Wannan mujallar ta tattauna yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba da kuma yadda za mu iya sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana yanzu.”

Awake! Mayu

“Muna tattaunawa da maƙwabtanmu ne game da wata matsala da ke ci mana tuwo a ƙwarya, wato, aikata laifi. Wasu suna ganin kamar idan aka ƙara masu tsaro, aikata laifi zai ragu. Mene ne ra’ayinka game da wannan batun? [Ka bari ya ba da amsa.] Shin ka san cewa Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa za a kawo ƙarshen aikata laifi? [Ka karanta Zabura 37:10, 11.] Wannan mujallar ta tattauna wannan alkawarin, kuma ta bayyana matakai da za mu iya ɗaukawa don mu kāre kanmu daga mutane masu aikata laifi.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba