Tsarin Ayyuka na Makon 1 ga Afrilu
MAKON 1 GA AFRILU
Waƙa ta 38 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 2 sakin layi na 10-16 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Luka 7-9 (minti 10)
Na 1: Luka 7:18-35 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Wace Sabuwar Al’umma Ce Allah Ya Ƙirƙiro a Ranar Fantikos, Kuma Me Ya Sa?—Gal.6:16; 1 Bit. 2:9 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Guji Dukan Ayyukan Sihiri?—td 37C (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 113
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Afrilu. Tattaunawa. Ka yi amfani da sakan 30 ko minti ɗaya don ka ambata dalilin da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Ta wajen yin amfani da jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro, ka ba masu sauraro dama su faɗi tambayar da za su yi da za ta sa maigidan ya so mujallar, kuma su faɗi nassin da za su karanta. Ka yi hakan ma da jigon da ke bangon gaba na Awake! da kuma wani talifi dabam da ke cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! idan da sauran lokaci. Ka sa a yi gwajin yadda za a gabatar da kowacce cikin mujallun.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Kun Taɓa Gwadawa Kuwa? Tattaunawa. Ta hanyar jawabi, ka ɗan yi bitar talifofi na kwanan nan da ke cikin Hidimarmu ta Mulki: “Yadda Za Mu Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi a Inda Ake Kasuwanci” (km 3/12), “Ku Taimaka wa Mutane Su Saurari Allah” (km 7/12), da kuma “Za Ku Iya Yin Wa’azi da Yamma?” (km 10/12). Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga bin shawarwarin da ke cikin talifofin nan.
Waƙa ta 75 da Addu’a