Tsarin Ayyuka na Makon 4 ga Maris
MAKON 4 GA MARIS
Waƙa ta 62 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 317 zuwa shafi na 319 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Markus 9-12 (minti 10)
Na 1: Markus 11:19–12:11 (minti 4 ko ƙasa hakan)
Na 2: Mene Ne ’Ya’yan Itacen da Aka Haramta?—td 44C (minti 5)
Na 3: Abin da Ya Sa Keɓe Kanmu ga Jehobah da Son Rai Yana Kawo Farin Ciki—Ayyukan Manzanni 20:35 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 7
Minti 10: Yadda Za A Gabatar da Mujallu a Watan Maris. Tattaunawa. Ka gaya wa masu sauraro su amsa tambayoyin da ke gaba: A ranakun Asabar da Lahadin da za ku rarraba takardar gayyatar mutane zuwa taron Tuna da mutuwar Yesu, a wane yanayi ne zai dace ku ba da mujallu? Mene ne za ku faɗa don ku ba da mujallu yayin da kuke gabatar da takardar gayyatar? Ko da yake gabatarwar da za a yi amfani da ita tana ɗauke da tambayar da za a yi da kuma nassi, ta yaya za ku iya taƙaita gabatarwarku? Ka sa a nuna yadda za a ba da kowace mujalla haɗe da takardar gayyatar.
Minti 10: Ka Amfana Daga Ƙasidar Examining the Scriptures Daily—2013. Tattaunawa. Ka ɗan tattauna nassin da aka ɗauko jigon shekara daga ciki da ke shafuffuka na 3-4 da kan maganar nan “How to Use This Booklet,” wato, “Yadda Za a Yi Amfani da Wannan Ƙasidar” a shafi na 5. Ka ba masu sauraro dama su faɗi lokacin da suka keɓe don tattauna nassin yini da kuma yadda suka amfana. A ƙarshe, ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su riƙa tattauna nassin yini na kowace rana.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Waƙa ta 119 da Addu’a