Tsarin Ayyuka na Makon 31 ga Disamba
MAKON 31 GA DISAMBA
Waƙa ta 60 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 288 zuwa shafi na 289 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Malakai 1-4 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 72
Minti 10: “Sabon Talifin da Zai Soma Fita a Cikin Hasumiyar Tsaro.” Jawabi. Ka sa a yi amfani da gabatarwar da ke shafi na 8 don a nuna yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta farko a watan Janairu.
Minti 10: Mene ne Muka Koya? Tattaunawa. Ka sa a karanta Luka 10:38-42. Ka tattauna yadda waɗannan ayoyin za su iya taimaka mana a aikin wa’azi.
Minti 10: Littattafai da Za a Ba da a Watan Janairu da Fabrairu. Tattaunawa. Ka tattauna wasu talifofi masu ban sha’awa a cikin littattafan da za a ba da, kuma ka sa a yi gwaji guda biyu a kan yadda za a ba da littattafan.
Waƙa ta 134 da Addu’a