Kada Ku Hana Kanku Samun Ɗalibai—Yadda Za Mu Yi Nazari da Mutane Ko da Muna da Hidimomi da Yawa
1. Me ya sa wasu masu shela suna jinkirin soma nazari da mutane?
1 Wasu masu shela suna jinkirin soma nazari da mutane domin suna da hidimomi da yawa. Koya wa mutane Littafi Mai Tsarki yakan ɗauki lokaci. Yin shirin nazari da ɗalibi da gudanar da nazarin da kuma taimaka wa ɗalibin ya shawo kan ƙalubale da yake fuskanta ayyuka ne da ke bukatar mu ba da lokacinmu. Manzo Bulus ya ce ya ba da ransa don ya taimaka wa mutane a Tasalonika su san Jehobah. (1 Tas. 2:7, 8) Ta yaya za mu iya gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki ko da muna da hidimomi da yawa a gabanmu?
2. Ta yaya ƙauna da muke wa Jehobah za ta shafi yadda muke amfani da lokacinmu?
2 Muna Bukatar Lokaci don Bauta wa Jehobah: A gaskiya, yin ibada ga Allah yana bukata mu keɓe lokaci. Alal misali, muna keɓe lokaci don halartar taro a kai a kai da zuwa wa’azi da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma addu’a. Ɗan’uwa mai aure wanda yake da ayyuka da yawa yakan yi marmarin keɓe lokaci don ya kasance da matarsa. Hakazalika, mu ma ya kamata mu “rifta zarafi” mu bauta wa Jehobah don muna ƙaunar sa, ko ba haka ba? (Afis. 5:15-17; 1 Yoh. 5:3) Yesu ya ce yin almajirai sashe ne mai muhimmanci sosai a bautarmu ga Jehobah. (Mat. 28:19, 20) Yin bimbini a kan abin da Yesu ya ce zai taimaka mana mu keɓe lokaci don gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.
3. Ta yaya za mu ci gaba da gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki idan yanayinmu ya sa ba ma cika samun zarafin fita wa’azi?
3 Me ya kamata mu yi idan ba ma samun zarafi saboda aiki ko ciwo mai tsanani ko kuma wasu ayyuka da suka shafi ibadarmu? Wasu ’yan’uwa da ba sa cika samun zarafi suna gudanar da nazari ta yin amfani da tarho ko kuma kwamfuta. Waɗanda ba su da zarafi don ciwo mai tsanani sukan gayyaci ɗalibansu zuwa gidajensu don su yi nazari da su. Wasu ’yan’uwa sukan shirya da wani ya yi nazari da ɗalibansu idan ba sa nan.
4. Wane albarka ne za mu samu idan muka saka hannu a aikin gudanar da nazari da mutane?
4 Manzo Bulus ya yi farin ciki sosai don ya yi amfani da lokacinsa da kuzarinsa wajen taimaka wa mutane su san Allah. (A. M. 20:35) Sa’ad da ya yi tunani a kan waɗanda ya taimaka musu su san gaskiya a Tasalonika, ya yi wa Jehobah godiya. (1 Tas. 1:2) Za mu yi farin ciki sosai idan ba mu bar yawan hidimomi su hana mu yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ba.