Tsarin Ayyuka na Makon 26 ga Nuwamba
MAKON 26 GA NUWAMBA
Waƙa ta 62 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 274 sakin layi na 10 zuwa shafi na 277 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Mikah 1-7 (minti 10)
Na 1: Mikah 3: 1-12 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Su Waye Za a Tayar Daga Matattu?—td 41A (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Muka San Cewa Jehobah Mai Amsa Addu’o’i Ne—1 Yoh. 5:14 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 56
Minti 5: Yadda Za Mu Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Ranar Asabar ta Farko. Ta wajen yin amfani da gabatarwar da ke shafi na huɗu, ka sa a gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta farko a watan Disamba. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su riƙa nazari da mutane.
Minti 10: Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu. Wani dattijo ya tattauna shafuffuka na 8 da 9 a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Nuwamba, 2012.
Minti 15: “Kada Ku Hana Kanku Samun Ɗalibai—Yadda Za Mu Yi Nazari da Mutane Ko da Muna da Hidimomi da Yawa.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka ɗan gana da wani da yake da ɗaliban da yake nazarin Littafi Mai Tsarki da su duk da hidimomi da yawa da ke gabansa.
Waƙa ta 73 da Addu’a