Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Disamba
MAKON 3 GA DISAMBA
Waƙa ta 128 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 278 zuwa shafi na 279 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Nahum 1 –Habakkuk 3 (minti 10)
Na 1: Habakkuk 2:1-14 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Muna Faɗan Gaskiya da Tabbaci?—2 Tim. 1:7, 8 (minti 5)
Na 3: A Ina Ne Za a Tayar da Matattu?—td 41B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 106
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Disamba. Tattaunawa. Ka ɗauki sakan 30 zuwa minti ɗaya ka tattauna dalilan da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Ka gabatar da jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro da kuma talifofi na farko, sai ka ba masu sauraro dama su faɗi tambayar da za su yi wadda za ta jawo hankalin mutane, sa’an nan su faɗi nassin da za su karanta. Ka yi hakan ma da jigon da ke bangon gaba na Awake! da kuma wani talifi dabam da ke cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! idan da sauran lokaci. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowace mujallar.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Labaran da Aka Samu Daga Ba da Warƙoƙi. Mai kula da hidima ne zai tattauna wannan sashen. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda mutane suka saurare su kuma suka karɓi warƙoƙin sa’ad da suke wa’azi a watan Nuwamba. Ka sa masu shela guda biyu da suka ji daɗin ba da warƙoƙi a wa’azi su yi gwaji a kan yadda suka yi hakan sa’ad da suke wa’azi gida-gida.
Waƙa ta 96 da Addu’a