Ka Kiyaye Azancinka
1. Mene ne jigon taron da’ira na shekara ta 2013, kuma mene ne manufar taron?
1 Yesu ya umurci almajiransa su yi ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu da dukan ransu da kuma dukan azancinsu. (Mat. 22:37, 38) An tsara taron gunduma na wannan shekarar da taron da’ira da kuma na musamman na shekara ta 2013 don su taimaka mana mu ƙara gyara halayenmu. Kamar yadda kuka sani, jigon taron gunduma ta shekara ta 2012, shi ne “Ka Kiyaye Zuciyarka!” Jigon taro na musamman na shekara ta 2013 kuma shi ne “Ka Kiyaye Lamirinka.” Sa’an nan jigon taron da’ira da za a soma a watan Janairu, 2013, shi ne “Ka Kiyaye Azancinka,” wanda aka ɗauko daga littafin Matta 22:37. An shirya wannan taron don ya taimaka wa kowannenmu ya inganta yadda yake tunani don mu riƙa yin tunanin da zai faranta wa Jehobah rai.
2. Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za a ba da amsoshinsu a taron?
2 Abin da Za A Tattauna: Yayin da muke sauraron jawabai a taron, zai dace mu mai da hankali ga amsoshin waɗannan tambayoyin da za su fitar da muhimman darussan:
• Ta yaya za mu guji bin ‘ra’ayin mutane’?
• Ta yaya za mu iya kawar da rashin sanin da ke mallakar hankalin marasa ba da gaskiya?
• Wane irin hali ne ya kamata mu kasance da shi?
• A waɗanne hanyoyi ne bimbini da ya dace zai amfane mu?
• Ta yaya za mu bar Jehobah ya gyara tunaninmu?
• Mene ne maza da mata da iyaye da yara za su yi don farin ciki ya kasance a cikin iyali?
• Ta yaya za mu kasance da shiri domin ranar Jehobah?
• Mene ne ake nufi da yin ɗamara don aiki?
• Wane amfani ne masu aikata abin da suka koya suke samu?
3. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci taron a kwanaki biyun, mu kasa kunne sosai yayin da ake gudanar da taron kuma mu yi amfani da darussan da muka koya?
3 Shaiɗan yana ƙoƙari sosai ya ɓata tunaninmu. (2 Kor. 11:3) Saboda haka, dole ne mu yi ƙoƙari mu kiyaye azancinmu don mu riƙa yin tunanin da zai faranta wa Jehobah rai. Ya kamata mu ci gaba da kasancewa da halin Kristi kuma mu yi tsayayya da wannan muguwar duniyar. ( 1 Kor. 2:16) Saboda haka, ku yi shiri don ku halarci taron a kwanaki biyun. Ku kasa kunne sosai. Yin amfani da darussan da za mu koya a taron zai taimaka mana mu yi ɗamara don aikin wa’azi.—1 Bit. 1:13.