Tsarin Ayyuka na Makon 6 ga Agusta
MAKON 6 GA AGUSTA
Waƙa ta 60 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 219 zuwa 221 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ezekiyel 24-27 (minti 10)
Na 1: Ezekiyel 24:15-27 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Tilas ne Dukan Kiristoci Su Zama Ministoci—td 31A (minti 5)
Na 3: Shin Ezekiel 18:20 Ya Ƙaryata Abin da ke Fitowa 20:5 Ne? (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 88
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Kun Shirya don Sabon Shekarar Makaranta? Tattaunawa. Ka ba ’yan’uwa dama su faɗi ƙalubalen da Kiristoci matasa za su iya fuskanta a makaranta. Ka bayyana yadda iyaye za su iya amfani da littattafan nan Watchtower Publication Index, da Young People Ask, da kuma wasu littattafanmu sa’ad da suke bauta ta iyali, don su koya wa yaransu yadda za su yi tsayayya wa gwaji da kuma bayyana bangaskiyarsu. (1 Bit. 3:15) Ka zaɓi kan magana ɗaya ko biyu, kuma ka tattauna wasu bayanai da ke cikin littattafanmu da za su iya taimakawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka taɓa yin wa’azi sa’ad da suke makaranta.
Minti 10: Bukatu na ikilisiya.
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Agusta. Tattaunawa. Ka ɗauki sakan 30 zuwa minti ɗaya wajen tattauna dalilan da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Ta wajen yin amfani da jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro da kuma talifofi na farko, ka sa masu sauraro su faɗi tambayar da za su yi wadda za ta jawo hankalin mutane, sa’an nan su faɗi nassin da za su karanta. Ka yi hakan ma da jigon da ke bangon gaba na Awake! da kuma wani talifi daga cikin mujallar idan da isashen lokaci. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowace mujallar.
Waƙa ta 97 da Addu’a